Jam'iyyar APC Ta Saki Jadawalin Yakin Neman Zabenta Na Shugaban Kasa
- Jam'iyyar APC ta shirya tsaf don kaddamar da yakin neman zaben shugaban kasa gadan-gadan
- Kwamitin kamfen jam'iyya a yau ta fitar da jerin jadawalin tafiye-tafiyen da za suyi wajen gamsar da yan Najeriya
- Tinubu ya yi alkawarin cewa zai magance matsalar tsaro cikin watanni shida da hawa mulki
Kwamitin yakin neman zaben jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta saki jadawalin yakin neman zabenta daga yanzu har zuwa ranar zaben 2023.
A cewar jadawalin, jam'iyyar za ta kaddamar da yakin neman zabena garin Jos, birnin jihar Plateau a ranar 15 ga Nuwamba, 2022, rahoton ChannelsTV.
Za ta kammala yakin neman zaben ranar 3 ga Febrairu a jihar Legas.
Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ne dan takaran shugaban kasa na APC kuma Kashim Shettima na zai yi masa mataimaki.
Kalli jadawalin:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
2023: Lokaci Ya Yi da 'Yan Arewa Zasu Biya Tinubu Alherin da Ya Musu, Shettima
Ɗan takarar mataimakin shugaban kasa a inuwar APC, Sanata Kashim Shettima, yace zaɓen 2023 wata dama ce ga 'yan arewa su saka wa Bola Tinubu bisa goyon bayan da ya nuna wa yankinsu a baya.
Jaridar Premium Times ta rahoto cewa Shettima ya yi wannan furucin ne yayin da ya ziyarci al'ummar Hausawa a Alaba-Rago, ƙaramar hukumar cigaba ta Iba, jihar Legas.
Shettima ya samu rakiyar gwamnan jihar, Babajide Sanwo-Olu, da takwaransa na jihar Kano, Dakata Abdullahi Ganduje, shugaban APC na Legas, Cornelius Ojelabi, da dukkan shugabannin 'yan arewa mazauna jihar.
Yace Tinubu ne ya yi fafutukar ɗora shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari a kujerar da yake kai a zaɓen 2015 ta hanyar bashi tulin kuri'u daga kudu maso yamma, ya sake maimaita haka a 2019.
Sanata Shettima ya ƙara da cewa Tinubu ne ya taimaka wa Atiku Abubakar ya nemi zama shugaban ƙasa a zaɓe lokacin da PDP ta kori tsohon mataimakin shugaban, haka ya sake yi wa Nuhu Ribado.
A kalamansa ya ce:
"Mu mutane ne masu karamci, ya kamata mu girmama alwashin da muka ci da alƙawarin da muka ɗauka. Wannan lokaci ne da 'yan arewa zasu biya ta hanyar goyon bayan Tinubu.
Asali: Legit.ng