Sarkin Ife Ya Angwance Da Amarya Ta 6 Cikin Wata Guda Kacal

Sarkin Ife Ya Angwance Da Amarya Ta 6 Cikin Wata Guda Kacal

  • Alkawari ya cika, Mai Martaba Ooni of Ife ya shiga daga ciki da tsaleliyar amaryarsa ta shida
  • Sarkin ya shiga auren sabbin amare a watan Satumba biyo bayan rabuwarsa da tsohuwar matarsa
  • Ana kyautata zaton cewa wannan ta shidan ba ita bace ta karshe, da yiwuwan sarkin ya kara

Kwanaki hudu kacal bayan auren Amarya ta biyar, Ooni (sarki) na garin Ife, Oba Adeyeye Ogunwusi, a ranar Litinin ya angwance da ta shida, Olori Temitope Adesegun.

Mai magana da yawun Sarkin, Moses Olafare, ya bayyana hakan a shafinsa na Facebook jiya.

Ya ce sabuwar amaryar Gimbiya ce daga kasar Ijebu, jihar Ogun.

An daura auren ne a Magodo, jihar Legas.

Watanni tara bayan matarsa ta biyu, Naomi Silekunola, ya sanar da rabuwarta da Sarkin, sarkin ya shiga auren sabbin Amare tun ranar 6 ga Satumba, 2022.

Kara karanta wannan

Karin Bayan: Manhajar WhatsApp Ta Dawo Aiki Bayan Daina Aiki

Kalli hotunan daurin auren:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ojaja
Sarkin Ife Ya Angwance Da Amarya Ta 6 Cikin Wata Guda Kacal Hoto: @thenation
Asali: Twitter

Oajaja
Sarkin Ife Ya Angwance Da Amarya Ta 6 Cikin Wata Guda Kacal Hoto: @thenation
Asali: Twitter

Olori6
Sarkin Ife Ya Angwance Da Amarya Ta 6 Cikin Wata Guda Kacal Hoto: @thenation
Asali: Twitter

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel