Minista Pantami Ya Lashe Lambar Yabon Kirkire-Kirkire na Ilmin Zamani
- Yau kamar kullum, Minista Farfesa Isa Ali Pantami ya samu lambar karramawa daga wajen Shugaba Buhari
- An karrama babban malamin Addinin kuma masanin ilimin zamani da lambar yabon ilmin cigaban zamani
- Shugaba Buhari ya ce sam bai yi zaben tumun-dare ba yayinda ya baiwa Malam Isa Ali Pantami mukami a gwamnatinsa
Ministan Sadarwa da Tattalin arzikin zamani, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami ya lashe lambar yabon kirkire-kirkire na ilmin zamani da gwamnatin tarayyar Najeriya tayi.
Shugaba Buhari ya gabatar masa da lambar yabon ne ranar Juma'a, 21 ga watan Oktoba, 2022 a taron karrama ma'aikatan gwamnati da suke nuna jajircewa.
Taron ya gudana ne a fadar shugaban kasa dake Aso Rock Villa, Abuja.
Ministan da kansa ya bayyana hakan a bidiyon da ya daura a shafinsa na Tuwita inda ya karbi lambar yabon.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A ranar Laraba, Shugaba Muhammadu Buhari ya taya Ministan Sadarwa da tattalin arzikin zamani, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami, murnar cika shekaru hamsin cir a duniya.
Buhari ya bayyana cewa Malam Pantami na daya daga cikin ma'aikata mafi kwazo, jajircewa da amfani a gwamnatinsa.
A jawabin da mai magana da yawun shugaban kasa Malam Garba Shehu ya fitar, Buhari ce zaben Pantami na daya daga cikin shawari mafi amfani da yayi a rayuwarsa, rahoton TheNation.
Farfesa Isa Pantami zai cika shekaru 50 da haihuwa a ranar Alhamis, 20 ga watan Oktoba, 2022.
An Ware Sheikh Isa Pantami Shi Kadai, An ba shi Kyautar Kasar Waje a Birnin Dubai
A baya mun kawo muku cewa Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani na Najeriya, Isa Ali Ibrahim Pantami ya samu lambar yabo saboda kokarin da yake yi a ofis.
Kamar yadda ya bayyana a Twitter a ranar Talata, 11 ga watan Oktoba 2022, Mai girma Ministan ya tashi da kyautar DWTC a Dubai a kasar UAE.
An ba Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami wannan lambar yabo ne la’akari da ayyukan da yake yi wa Najeriya tun da ya zama Ministan sadarwa a 2019.
Jaridar Science Nigeria tace an karrama Isa Pantami bayan ya gabatar da jawabinsa a game da yadda za a tafi da kowa a harkar sadarwa na zamani.
Pantami ya yi jawabin ne a taron GITEX wanda ake yi yanzu haka a dunkullaliyar kasar Larabawa.
Asali: Legit.ng