Yau Bayan Sallar Juma'a Zan Bayyanawa yan Najeriya Manufata Ta Gyara Kasar, Tinubu

Yau Bayan Sallar Juma'a Zan Bayyanawa yan Najeriya Manufata Ta Gyara Kasar, Tinubu

Dan takaran shugaban kasan Najeriya a zaben 2023 karkashin jam'iyyar All Progressives Congress APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana cewa yau yan Najeriya zasu fahimci manufarsa.

Tinubu yace bayan Sallar Juma'a misalin karfe 3 na rana zai bayyana tsarin da yayi na fidda Najeriya daga halin da take ciki idan ya samu nasara a zaben 2023.

Tsohon gwamnan na Legas ya bayyana hakan ne a shafinsa na Tuwita.

Yace:

"Yau misalin karfe 3 na rana. Zan bayyana shirin da nayi don gyara Najeriya. Kuyi tarayya dani."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel