Kotun Daukaka Kara Ta Wanke Nnamdi Kanu, Ta Yi Watsi da Karar Gwamnati

Kotun Daukaka Kara Ta Wanke Nnamdi Kanu, Ta Yi Watsi da Karar Gwamnati

  • Shugaban kungiyar rajin kafa kasar Biafra, Nnamdi Kanu ya samu nasara kan gwamnatin tarayya
  • Kotun daukaka kara dake zamanta a Abuja ta yi watsi da zargin ta'addanci da gwamnatin tarayya keyi masa
  • Kotun Ta Umurci Gwamnati Ta Sake Shi saboda an saba doka wajen daukoshi da akayi daga Kenya

Abuja - Kotun daukaka kara dake zamanta a Abuja ta yi watsi da zargin ta'addanci da gwamnatin tarayya keyi kan shugaban kungiyar rajin kafa kasar Biafra, Nnamdi Kanu.

Alkalan kotun a ranar Alhamis su uku su kara da cewa dauko Nnamdi Kanu da gwamnati tayi daga kasar Kenya ya sabawa doka.

Lauyan Kanu, Ifeanyi Ejiofor, a jawabin da ya fitar a shafinsa na Tuwita ya bayyana cewa:

"Kotu tace ba daidai bane dauko Mazi Nnamdi Kanu daga Kenya. Kotu tace hakan ya sabawa dokokin duniya kuma babu wani gamsasshen hujjan yin hakan ko da ko a Najeriya ne."

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Kotun Daukaka Kara Ta Sallami Shugaban IPOB, Nnamdi Kanu, Ta Kallubalanci Hukuncin Babban Kotu

"An amince mu daukaka kara, an wanke Onyendu Mazi Nnamdi Kanu. Mun yi nasara."
Kanuu
Kotun Daukaka Kara Ta Wanke Nnamdi Kanu, Ta Yi Watsi da Karar Gwamnati

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida