Tsohon Shugaban Jam'iyyar PDP Da Yace PDP Za Tayi Shekaru 40 Kan Mulki Ya Mutu

Tsohon Shugaban Jam'iyyar PDP Da Yace PDP Za Tayi Shekaru 40 Kan Mulki Ya Mutu

  • Jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party PDP tayi babban rashin daya daga cikin manyan iyayenta
  • Vincent Ogbulafor ya kasance babban sakataren jam'iyyar lokacin mukin marigayi Umwar Musa Yar'adua

Sakataren kasa farko kuma tsohon shugaban uwar jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Chief Vincent Ogbulafor, ya rigamu gidan gaskiya.

Iyalan Ogbulafor sun bayyana cewa ya mutu ne ranar Alhamis sanadiyar jinya da yayi, tahoton ThisDay.

Ya mutu yana mai shekaru 73 a duniya.

Ogbular
Tsohon Shugaban Jam'iyyar PDP Da Yace PDP Za Tayi Shekaru 40 Kan Mulki Ya Mutu

Ogbulafor ya kasance Sakataren Jam'iyyar PDP na farko sannan ya zama Shugaban uwar jam'iyyar bayan rikicin da ya barke tsakanin Sanata Sam Egwu da Shugaban majalisar dattawa na lokacin, Anyim Pius Anyim.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Allah Ya Yi Wa Tsohon Shugaban Jam'iyyar PDP Na Ƙasa Rasuwa A Canada

Da rikici tayi kamari aka tilasta masa murabus daga kujerar.

Daga baya ya zama Minista kuma aka gurfanar da shi kan zargin almundahanar kudin gwamnati.

Ogbulafor ya shahara da jawabin da yayi na cewa PDP za ta kwashe shekaru 40 a mulki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel