Gwamnatin Tarayya Ta Bada Hutu Ranar Litinin Don Murnar Eid-l-Maulud

Gwamnatin Tarayya Ta Bada Hutu Ranar Litinin Don Murnar Eid-l-Maulud

  • Gwamnatin tarayya tace ma'aikata su zauna gida ranar Litinin su huta albarbakin ranar Maulidi
  • Minista ya yi kira ga Musulmai su kwaikwayi kyawawan dabi'un Annabi kamar yadda ya karantar
  • Kowace shekara, Musulmai a fadin duniya na murnar zagayowar ranar 12 ga watan Rabi'ul Awwal

Abuja - Gwamnatin tarayya ta ayyana ranar Litinin, 10 ga watan Oktoba matsayin ranar hutu don Eidul-Maulid na murnar haihuwar Annabi Muhammadu (SAW).

Ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola, ya bayyana hakan a jawabin da Sakataren din-din-din na ma'aikatar, Shuaib Belgore ya fitar madadinsa ranar Alhamis.

Aregbesola ya shawarci yan Najeriya su yi koyi da dabi'un Annabi Muhammadu na soyayya, hakuri, ibadah don samar da zaman lafiya a doron kasa.

Wani sashen jawabin yace:

"Aregbesola ya kwadaitar da yan Najeriya, musamman Musulmai, su kauracewa fadace-fadace, saba doka da kuma aikata laifuka."

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Bola Ahmed Tinubu Ya Diro Najeriya Bayan Kwashe Kwanaki a Turai

Aregbe
Gwamnatin Tarayya Ta Bada Hutu Ranar Litinin Don Murnar Eid-l-Maulud Hoto: NTA
Asali: UGC

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida