Fulani Sun Koka Kan Yadda Ake Cigaba da Yi Musu Kisan Gilla

Fulani Sun Koka Kan Yadda Ake Cigaba da Yi Musu Kisan Gilla

  • Fulani dai na cigaba da fuskantar razani ni a muhallansu da ke jihohi da dama a Najeriya
  • Domin ko da wannan rana ta Alhamis, wata ƙungiyar Fulani ta yi Alla-wadai da kisan gillar da aka yi wa Fulani a jihohi guda biyu na Najeriya
  • Ƙungiyar ta kuma sha alwashin cewa, ba za ta sarara ba wajen bin kadin mutane da suka gamu da wannan ibtila’i

Wata ƙungiyar kabilar Fulani mai suna Fulbe Global Development Initiative (FGDRI) ta koka game da kuɗin goro da ake yi wa fulani tare da kashe ba tare da nuna tausayi ba.

Shugaban wannan ƙungiya, Salim Musa Umar, a ranar Alhamis ɗin, ne ya bayyana haka ga manema labarai a jihar Kaduna.

Ya nuna fargabarsa wajen yiwuwar faruwar abin da ya taɓa faruwa a ƙasar Rwanda, wanda a cewarsa ba zai haifar wa da Najeriya ɗa mai ido ba.

Kara karanta wannan

Lokaci Ya Yi: Wata Budurwa Yar Shekara 18 Dake Kan Ganiyarta Ta Mutu a Hotel

Fulani
Fulani Sun Koka Kan Yadda Ake Cigaba da Yi Musu Kisan Gilla

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ƙungiyar ta nuna alhininta game da kisan gilla da aka yi wa makiyaya Fulani a Bali da ke jihar Taraba da kuma Birnin Gwari da ke jihar Kaduna, rahoton Vanguard.

Ta bayyana cewa wannan ba wai sabon abu ba ne face misali ne na irin yunƙurin shafe Fulani da ake yi a wasu jihohi na ƙasar nan.

“Ko shakka ba ma yi, cewa Fulani mutane masu son zaman lafiya, masu mutunta mutane da ke ba da gudunmawa ga kuɗaɗen shiga na cikin gida ga ƙasar nan, musamman ɓangaren noma wanda ya dogara ne da ayyukan makiyayan nan,”

....a cewar shugaban ƙungiyar.

Sannan ƙungiyar ta miƙa godiyarta ga jami’an tsaro da suka yi hanzari wajen kai agaji wurin tare da kame mutane huɗu da ake zargi da haddasa wannan kashe-kashe a jihar ta Taraba.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Bayan Shafe Watanni Uku, Yan Bindiga SUn Saki DPOn Yan Sandan Da Suka Sace

Ya kuma gode wa gwamnatin jihar Kaduna na ɗaukar matakin da ya dace.

Shugaban ƙungiyar ta FGDRI yace:

“Muna kira ga gwamnatocin ƙasa da ta jihohi da su hanzarta wajen kawo wa waɗanda abin ya shafa agaji, saboda tuni makasan suka yi awon gaba da dabbobinsuu da su ne kaɗai abin da suka dogara da su.
Haka kuma wannan ƙungiya za ta sa ido game da bincike na jami’an tsaro tare da bindiddigi domin samar da adalci ba tare da nuƙusani ba,”

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida