An Tabbatar Da Mutawar Wasu Yan Gida Daya Bayan Cin Amala a Jihar Kogi
- Wasu Yan gida daya sun ce ga garin ku nan bayan lodan Amala da dare a jihar Kogi, Arewa maso tsakiya
- An kaddamar da bincike kan garin alabon da akayi amfani da shi wajen tuka tuwon Amalan
- Irin wannan abu ya faru watan Agusta duk a jihar Kogi inda wasu suka mutu bayan cin Amala
Kogi - Al’ummar garin Mopa da ke karamar hukumar Mopa-Muro a jihar Kogi sun tashi da alhini tare da jimamin haɗi da makokin wasu ƴan gida daya su huɗu da suka hadu da ajalinsu bayan cin tuwon Amala.
Rahotanni da suke fitowa daga garin sun ce wadanda lamarin ya rutsa da wanda suka mutun ne a tsakanin ranar Juma’a 30 ga watan Satumba da kuma Lahadi 2 ga watan Oktoba na shekarar da muke ciki.
Cikin wanda suka fara mutuwa akwai jigon gidan, Pa. Motilewa, da ƴa'ƴansa da kuma matansa su biyu, sai wata yarinya da aka ce ƴar danginsu ce.
Daga cikin ‘ƴan gidan da suka rasu, akwai wata mai suna Motun wadda malama ce a garin. Amma uwar gidan Mr. motilewa, ta tsira daga wanan iftila’in.
Lamarin dai ya jefa mazauna garin da ma daukacin wanda ke kusa garin cikin alhini, fargaba da rudani, inda da dama daga cikin ƴan garin ke kira da a gudanar da bincike kan mutuwar yan gida ɗayan nan.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Jaridar PUNCH ta rawaito cewa dangin sun shirya abincin (Amala) wanda ake sarrafashi da garin rogo sannan suka haɗa da miyar Fufu.
An ce sun shanya sandar rogon a rana tsawon wasu kwanaki. Daga baya kuma suka nika busasshen sandar rogo ɗin yai laushi, wanda da shi aka yi amfani wajen sarrafa Amala wanda suka ci ranar Alhamis kafin su kwanta.
Wani ganau ya ce wadanda lamarin ya rutsa da su sun yi rashin lafiya cikin dare kuma an yi kokarin kwantar da su. Amma ɗan ƙaramin ɗan gidan ya rasu ranar Juma'a, sai kuma sauran ƴan gidan a ranar Asabar.
Wakilin jaridar PUNCH ya samu labarin cewa an kai sauran Asibitin ECWA da ke Egbe domin samun kulawar likitoci. Duk da haka, babbar ƴa a gidan, Motun, ta ce ga garinku da misalin karfe 3 na daren Lahadi. Mahaifin kuma ya rasu a ranar Lahadin nan.
Har zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto, mahaifiyar mai suna Molomo, tana raye a asibiti kuma ana sa ido sosai.
An bayyana cewa al’ummar yankin na zargin mutuwar tasu ne da wani abu dan gane da garin rogo, kuma sun dakatar da binne su domin gudanar da cikakken bincike domin gano musabbabin mutuwarsu.
“Mun yi mamaki so sai ban taba ganin abu makamancin haka ba. Muna zargin cewa wata kila wani ya sanya guba a abincin. Don me? Ba za mu iya fada ba. Ina cikin rudani kuma ina jin zafi. Wannan ya yi yawa da ba za a iya jurewa ba,” in ji wani daga cikin dangin dagin mamatan.
A watan Agustan 2022, mutane biyar sun rasa rayukansu bayan sun ci abincin (Amala) da aka shirya a gidansu da ke Usugnwe-Okaito, a karamar hukumar Okehi ta jihar Kogi.
A halin da ake ciki, gwamnatin jihar Kogi ta bai wa mazauna garin na Mopa tabbacin aniyar ta na sanin tushen lamarin.
Da yake jawabi yayin ziyarar ta’aziyya da ya kai fadar Elulu na Mopa a madadin gwamnan, kwamishinan yada labarai da sadarwa na jihar, Kingsley Fanwo, ya ce gwamnan ya yi bakin ciki da faruwar lamarin, yana mai tabbatar wa jama’a cewa:
“Ba za a bar kafa kan lamarin ba ba tare da an tona asirin da ya sabbaba mutuwar wadanda abin ya shafa.”
“Gwamnan ya umurci hukumomin tsaro da hukumomin lafiya da su binciki tushen lamarin. Ina so in tabbatar wa mai martaba cewa za a bayyana rahotan bincikensu a bainar jama’a kuma a dauki matakan da suka dace,”
Asali: Legit.ng