Wutar Lantarki Ta Dauke A Najeriya Gaba Daya Da Safiyar Nan, 0 Megawatt
Injinan Wutan lantarkin Najeriya sun durkushe zuwa 0Megawatt kaf misalin karfe 10:51 na safiyar Litnin, 26 ga watan Satumba, 2022, rahoton Daily Trust.
Hakan ya sabbaba rashin lantarkin da ake fama da shi a fadin Najeriya.
A bisa bayanan da aka samu, tashar raba wutan lantarkin TCN Afam IV kadai ke aiki amma babu wuta ko daya.
Kamfanonin raba lantarki (DisCos) sun sanar da kwastamominsu bisa aukuwar wannan lamari.
Misalin jami'in yada labaran kamfanin lantarkin Enugu EEDC yace a fadin tarayya ake fama da matsalar rashin wutan.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
A cewarsa:
"Kamfanin raba wutar lantarkin Enugu (EEDC) na sanar da kwastamominta cewa lalacewar wutan da ya auku misalin karfe 10:51 na safiyar yau, 26 ga Satumba, 2022, ya yi sanadiyar dauke wutan da ake fama da shi a fadin tarayya."
Hakazalika kamfanin wutan Benin BEDC ya sanar da mazauna yankin Edo, Delta, Ekiti, Ondo da kewaye.
Asali: Legit.ng