Tirkashi: Sunan Sanata PDP, Chimaroke Nnamani Ya Fito Cikin Kwamitin Kamfen APC
- Sunan daya daga cikin Sanatocin jam'iyyar adaw ata PDP ya bayyana cikin kwamitin kamfen APC
- Wannan ya zama sabon kalubale ga jam'iyyar PDP yayinda suke fama da rikicin cikin gida
- A Agusta, Tsohon Gwamnan jihar Enugu, Dr. Chimaroke Nnamani ya kare Bola Tinubu daga masu sukarsa
Jigon jam'iyyar Peoples Democratic Party PDP kuma Sanata mai wakiltar mazabar Enugu Ta Gabas, Chimaroke Nnamani ya samu shiga cikin kwamitin yakin neman zaben jam'iyyar All Progressives Congress, APC,.
Jam'iyyar APC ta saki sunayen mutanen da zasu taka rawar gani wani ganin tayi nasara a zaben 2023.
Wani suna guda daya da akayi mamakin gani shine na tsohon gwamnan jihar Enugu, Chimaroke Nnamani.
Nnamani ne lamba na 350 kuma zai yi aiki a matakin karamar hukuma.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
2023: Babban Jigon PDP Ya Jinjinawa Bola Tinubu, Ya tsokano ‘Yan adawan APC
A wata Agusta, Chimaroke Nnamani ya yabawa ‘dan takaran shugaban kasa na APC, Asiwaju Bola Tinubu, yana mai tir da masu sukarsa saboda halin lafiyarsa.
A wasu dogoyen bayanai da ya yi a shafin Twitter a ranar 10 ga watan Agusta 2022, Chimaroke Nnamani yace ba a taba yin gwamna irin Bola Tinubu ba.
Sanatan na gabashin Enugu ya bada labarin irin rawar da Tinubu ya taka a lokacin yana gwamnan Legas, a lokacin Nnamani yana Gwamna a jihar Enugu.
Nnamani yake cewa Tinubu ya kawo tsare-tsaren da suka taimaka ya gyara harkar shari’a, ilmi, kiwon lafiya, kuma yayi aiki da wadanda ba Legasawa ba.
Asali: Legit.ng