Ba'a Taba Lalatacciyar Gwamnati Irinta Ta Buhari A Tarihin Najeriya Ba, Buba Galadima
- Sakataren kwamitin amintattun jam'iyyar NNPP ya yi kira da yan Najeriya suyi addu'a Buhari ya karasa wa'adinsa ya tafi lafiya
- Alhaji Buba Galadima ya bayyana cewa a gaban Buhari aka abubuwan da basu dace amma bai iya komai
- Buba Galadima ya kasance kakakin kamfen Atiku a PDP a 2019 amma yanzu ya koma jam'iyyar NNPP
Birnin Kebbi - Tsohon na kusa da Shugaba Muhammadu Buhari, Injiniya Buba Galadima, ya siffanta gwamnatin APC a matsayin mafi lalaci a tarihin Najeriya.
Vanguard tace Buba Galadima ya bayyana mata hakan ne a hirar da yayi a Birnin Kebbi inda dan takarar jam'iyyar New Nigeria Peoples Party, Rabiu Musa Kwankwaso, ya kai ziyara.
Galadima yace lamarin Buhari da ban tausayi saboda munanan abubuwa na faruwa a gabanshi amma ba zai iya komai ba.
Yace a wa'adin Buhari na farko, sun yi tunanin yan Najeriya basu fahimceshi bane, amma duk ya kunyatasu.
Yace:
"Addu'ata daya yanzu kuma ina kira ga yan Najeriya suyi shine ya samu ya karasa mulkinsa cikin lafiya, saboda gwamnatinsa za ta zama mafi muni a tarihin Najeriya."
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Game da yakin neman zabe kuwa, Buba Galadima, wanda shine sakataren kwamitin amintattun jam'iyyar yace NNPP da zama zakaran gwajin dafi a Najeriya yanzu.
Yace yadda suke samun kyakkyawan tarba daga wajen yan Najeriya a ziyarce-ziyarcen da suke kaiwa Arewa da Kudu, yana da tabbacin Kwankwaso zai yi nasara a 2023.
UNGA77: Shugaba Buhari Yayi Bankwana da Shugabannin Kasashen Duniya
A ranar Larabar da ta gabata shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shaidawa shugabannin duniya cewa gwamnatinsa ta kuduri aniyar samar da tsarin zabe na gaskiya da adalci wanda zai kawo sabon shugaban kasa a shekara mai zuwa.
Ya kara tabbatar da cewa sabuwar fuska ce za ta wakilci Najeriya a taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 78 a shekarar 2023 mai zuwa.
Buhari ya yi wadannan kalaman ne a jawabinsa na karshe a matsayin shugaban kasa a taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 77 da aka gudanar a birnin New York na kasar Amurka.
Asali: Legit.ng