Jerin Gwamnoni 4, Ministoci 8, Da Wasu Manya 4 Da Suka Yiwa Buhari Rakiya Amurka
Shugaba Muhammadu Buhari ya tafi birnin New York, kasar Amruka don halartan taron gangamin majalisar dinkin duniya.
Wakilin kamfanin dillancin labaran Najeriya NAN ya ruwaito cewa Shugaba Buhari ya dira babbar tashar jirgin JF Kennedy ne misalin karfe 6:20 na yamma.
Shugaban kasan ya samu tarba daga wajen Ministan harkokin wajen Najeriya, Geoffrey Onyeama; wakilin Najeriya a majalisar dinkin duniya, Tijjani Muhammad-Bande da jakadan Najeriya zuwa Amurka, Dr Mrs Uzoma Emenike, dss.
Shugaba Buhari zai gabatar da jawabin farko na ranar Laraba ga shugabannin duniya misalin karfe 2 na rana (agogon Najeriya).
Legit.ng Hausa ta tattaro muku jerin wadanda suka raka Buhari New York
Gwamnoni
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum
Gwamnan jihar Zamfara, Muhammadu Bello Matawalle
Gwamnan CBN, Godwin Emefiele
Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwoolu
Ministoci
Ministan Aikin Noma, Mahmoud Mohammed
Ministan masana'antu da kasuwanci, Otunba Niyi Adebayo
Ministan Ilimi, Adamu Adamu
Ministan Sufuri Muazu Jaji
Ministan Lafiya, Osagie Ehanire
Ministan harokin wajen Najeriya, Geofreey Onyeam
Ministar Jinkai, Walwala da jin dadin al'umma Sadiya Farouq
Ministar Kudi, Zainab Shamsuna
Saura
Shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari
Tsohon Sakataren gwamnatin tarayya, Babagana Kingibe
Shugaban hukumar EFCC, AbdulRashid Bawa
Shugabar hukumar NIDCOM, Abike Dabiri
Mai Baiwa shugaban kasa kan tsaro, Babagana Munguno
Mai Magana da Yawun shugaban kasa, Femi Adesina
Asali: Legit.ng