Gwamnatin Birtaniya ta saki sunayen yan Najeriya 56 da suka mutu suka bar dukiya ba’a san yan uwansu ba

Gwamnatin Birtaniya ta saki sunayen yan Najeriya 56 da suka mutu suka bar dukiya ba’a san yan uwansu ba

  • An bayyana sunayen wasu yan Najeriya 56 da suka mutu suka bar dukiya a Birtaniya
  • Wasu sunayen dake cikin jerin sun mutu tun shekarar 1998 kuma har yanzu babu wanda ya gaji dukiyarsu
  • Gwamnatin Birtaniya ta rike dukiyar tana sauraron wani magaji yazo an damka masa

Gwamnatin kasar Birtaniya ta saki bayanai kan mutane 6,743 da suka mutu suka bar dukiya babu magaji.

Da cikin sunayen akwai na yan Najeriya 56 wadanda suka mutu tsakanin shekarar 1996 da 2021 a kasar.

A dokar kasar, za’a ajiye dukiyoyin tsawon shekaru 30 kafin gwamnati ta mallake.

Dukiya
Gwamnatin Birtaniya ta saki sunayen yan Najeriya 56 da suka mutu suka bar dukiya ba’a san yan uwansu ba
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sunayen wadanda ke kan jadawalin

A cewar ofishin baitil malin kasar Birtaniya, daya daga sunayen akwai Julius Taiwo wanda ya mutu tun ranar 19 ga July, 1995 a Derby Derbyshire.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar PDP Ba Ta Dan Takaran Gwamna a Zaben 2023, Kotu Ta Soke Zaben Fidda Gwani

A cewar BusinessDay, Wani sanannen suna a jeringiyar sunayen shine Victor Adedapo Olufemi Fani-Kayode wanda ya mutu ranar 15 ga Agusta, 2001 a Birmingham.

Kalli jerin sunayen a nan da nan

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida