Atiku Tun Yana Dan Shekara 15 Ya Ginawa Mahaifiyarsa Gida, Alaba Yusuf
- Mamban kwamitin yakin neman zaben Atiku-Okowa ya bayyana cewa Atiku fa ya dade yana da arziki
- Alaba Yusuf yace Atiku ya san talauci kuma ya san wadata saboda haka zai san yadda zai taimakawa yan Najeriya
- Alhaji Atiku Abubakar shine dan takaran kujerar shugaban kasa karkashin jam'iyyar adawa ta PDP
Daya daga cikin masu magana da yawun kwamitin yakin zaben kujerar shugaban Najeriya na jam'iyyar Peoples Democratic party (PDP), Alaba Yusuf, yace dan takaransu, Atiku Abubakar, ikon Allah ne.
Alaba yace Atiku na da karfin tsamo miliyoyin yan Najeriya daga bakin talaucin da suke ciki.
Ya bayyana hakan ne a shirin Sunrise Daily na tashar ChannelsTV yayinda yake bayani kan yadda zai fito da yan Najeriya daga kangin talauci, DailyTrust ta shaida.
Yace:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Atiku fa yana dan shekara 11 mahaifinsa ya rasu, ya ginawa mahaifiyarsa gida yana dan shekara 15."
"Abinda nike nufi shine Atiku babba ne. Ya san talauci kuma ya fahimci ma'anar talauci. Mutumin da ya canza rayuwarsa da na al'ummarsa zai yi sauya tattalin arzikin kasa."
"Atiku na da kamfanoni masu baiwa mata tallafi. A ganinsa idan ya taimakawa mata, ka taimakawa kasa saboda kowani iyali zai amfana."
Yusuf ya siffanta Atiku matsayin mutumin dake da zurfin ilmin kasuwanci.
Atiku Abubakar: Abubuwan da Zan Yi a Kwanaki 100 na Farko da Zan Yi a Ofis
Atiku Abubakar yace zai fito da wani asusun Dala biliyan 10 domin ya farfado da tattalin arziki.
A ranar Talata, 13 ga watan Satumba 2022, Daily Trust ta rahoto Alhaji Atiku Abubakar yana bayanin yadda zai fara mulki idan ya zama shugaban kasa.
‘Dan takaran yake cewa a kwanaki 100 na farko da zai yi a kan mulki, zai maida hankali wajen taimakawa matsakaita da kananan ‘yan kasuwan kasar nan.
Rahoton yace Atiku Abubakar ya yi wannan bayani ne wajen gabatar da manufofin tatalin arzikinsa a gaban ‘yan kasuwa a taron da LCCI ta shirya a garin Legas.
Asali: Legit.ng