Tukur Mamu Na Daukan Nauyin Yan Ta'adda, Inji Hukumar DSS
- Hukumar DSS ta bayyana cewa Tukur Mamu Infoma ne ga yan bindiga kuma yana kai musu bayanai
- Hakazalika Ana zargin dan jaridan da kaiwa yan ta'addan da suka addabi arewa kaya da kudade
- Hukumar DSS ta shigar da kara kotu don a bata daman cigaba da rike Tukur Mamu don kammala bincike
Hukumar tsaron farin kaya DSS ta tuhumci mai gidan jaridar Desert Herald, Tukur Mamu, da laifin daukan nauyin yan ta'adda a Najeriya.
Hukumar ta tsaron tace Tukur Mamu, wanda ya shahara da taya iyalan wadanda aka sace a harin jirgin kasa cinikin kudin fansa da yan bindiga yana baiwa yan ta'addan gida da waje kudade.
DSS ta tuhumci Mamu da baiwa kungiyoyin yan ta'adda bayanai, wanda hakan ke tsananta matsalar tsaro a Najeriya.
Hakan na kunshe cikin karar da hukumar ta shigar kotu kan Mamu ranar 12 ga Satumba, 2022.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
A rahoton da kamfanin dillancin labaran NAN ya koro yace DSS ta rubuta a karar da shigar kotu cewa:
"Binciken farko-farko da aka gudanar sun nuna cewa ana tuhummarsa da kaiwa yan ta'addan kayayyaki, yana taimaka musu da kudi."
"Wanda ake zargin (Mamu) yana basaja da aikin jarida wajen taimakawa kungiyoyin yan ta'adda na gida da na waje."
"Wannan abu da yake yi ya haddasa mutuwar jami'an tsaro da dama a yankin Arewa maso tsakiya da Arewa maso gabas."
"Wanda ake zargin (Mamu) a lokuta da dama ya baiwa yan bindiga bayanai wanda ke tsananta rikici a Najeriya."
Kotu Ta Baiwa Hukumar DSS Ikon Cigaba da Rike Tukur Mamu Tsawon Watanni 2
Babbar kotun tarayya dake zaman a birnin tarayya Abuja ta baiwa hukumar tsaron farin kaya DSS izinin cigaba da tsare Tukur Mamu, na tsawon watanni biyu.
Hukumar DSS a ranar 12 ga Satumba ta bukaci kotu ta bata damar kammala bincikenta kan Mamu.
A karar mai lamba FHC/ABJ/CS/1617/2022 lauyan DSS, Ahmed Magaji, ya bukaci karin kwanaki 60.
Alkali Nkeonye Maha, a hukuncin da yanke ranar Talata, 13 ga Satumba, ya baiwa DSS daman cigaba da tsareshi
Asali: Legit.ng