Kada Wani Bakin Fata Yayi Jimamin Mutuwar Sarauniya Elizabeth, Trevor Sinclair
- Da alamun ba kowa ke jin dadin yadda duniya ta dau dumi bisa mutuwar Sarauniyar Ingila, Elizabeth II ba
- Wani tsohon dan kwallon Ingila, Trevor Sinclair, ya ce kada bakaken fata suyi wani jimami bisa mutuwarta
- Sinclair yace a gaban idon sarauniyar aka rika cin mutuncin bakaken fata da nuna wariyar launin fata
Tsohon dan kwallon kasar Ingila, Trevor Sinclair, ya sha suka bayan jawabin da ya saki a shafinsa na Tuwita inda yayi kira ga bakaken mutane kada suyi jimamin mutuwar Queen Elizabeth.
Sinclair a jawabinsa yace haka ta zuba ido karkashin mulkinta aka rika nunawa bakake wariyar launin fata.
DailyMail ta ruwaito cewa sabanin abinda sauran taurarun kwallo keyi na tura sakonnin ta'aziyya, Sinclair ya caccaki masarautar Ingila.
Yace:
"An soke wariyar launin fata a Ingila a shekarun 1960's amma aka bari hakan ya cigaba saboda haka ta wani dalili bakaken fata zasuyi jimami"
Dan kwallon tuni ya goge shafinsa na Twitter.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Gidan Jaridar talkSports tayi martani
Kamfanin jaridar talkSports, inda Sinclair ke aikin sharhi kan harkar kwallo ya barranta kansa daga jawabin Sinclair.
A cewar kamfanin:
"Muna ta kokarin tuntubar Trevor Sinclair sakamakon ra'ayinsa da ya bayyana a shafinsa na Tuwita."
“talkSPORT ba ta goyon bayan wannan ra'ayi kuma tana binciken lamarin."
Ni Da Yan Najeriya Na Jimamin Mutuwar Mahaifiyarka, Buhari ga Sarkin Ingila
Shugaba Muhammadu Buhari ya aike sakon ta'aziyya ga sabon Sarkin Ingila bisa mutuwar Sarauniya Elizabeth, mahaifiyarsa da kuma tayashi murnar hawa mulki.
A sakon da ya wallafa a shafinsa na Tuwita, Shugaba Buhari yace tarihin Najeriya a matsayin Ƙasa ba zai taɓa cika ba, ba tare da an tabo babin Sarauniya Elizabeth ba.
Mun kawo muku labarin rasuwar sarauniyar Ingila Elizabeth II bayan 'yar gajiriyar rashin lafiya da aka sanar ta yi a ranar Alhamis 8 ga watan Satumba, 2022.
Rahotanni daga majiyoyi sun shaida cewa, masarautar Ingila ta tashi bakin labarin jirkicewar lafiyar sarauniya, lamarin da yasa likitoci ke kai komo a kanta.
Asali: Legit.ng