Ni Da Yan Najeriya Na Jimamin Mutuwar Mahaifiyarka, Muna Maraba Da Hawanka Mulki: Buhari ga Sarkin Ingila
- Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari yace yaji baƙin ciki matukar gaske da samun labarin Rasuwar Sarauniyar Elizabeth na biyu
- Buhari yace kashi 90% na yan Najeriya basu san wani mulki ba illa na Sarauniyar ta Ingila
- Shugaban kasan ya yi laale marhabun ga hawa mulkin babban 'danta Yarima Charles
Shugaba Muhammadu Buhari ya aike sakon ta'aziyya ga sabon Sarkin Ingila bisa mutuwar Sarauniya Elizabeth, mahaifiyarsa da kuma tayashi murnar hawa mulki.
A sakon da ya wallafa a shafinsa na Tuwita, Shugaba Buhari yace tarihin Najeriya a matsayin Ƙasa ba zai taɓa cika ba, ba tare da an tabo babin Sarauniya Elizabeth ba.
A cewar jawabin:
"Ni da iyalai na, da Al'umman Najeriya sama da Miliyan Ɗari Biyu, sun ji ɓacin Rai matuka-gaya na Rasuwar Sarauniya Elizabeth, wanda hakan ya kawo ƙarshen Mulki ta na tsawon shekaru Saba'in mai cike da abin sha'awa da babu irin sa.
"Mulkin Marigayiyar shine kadai Masarauta mai Girma a Turai da kashi Chas'in cikin Ɗari na Al'umman mu suka sani."
"Shugaba Buhari yayi Maraba da Mai Girma Yarima Charles bisa Gadon Mulki da yayi wanda hakan na daidai da tsarin Masarautan, ya kuma yi Addu'an ganin ci gaba da samun karin ingantuwar Dangantaka da alaka tsakanin kasashen biyu a yayin mulkin Yarima Charles na Uku."
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Sarauniyar Ingila, Elizabeth II Ta Kwanta Da, Ta Rasu Tana da Shekaru 96
Mun kawo muku labarin rasuwar sarauniyar Ingila Elizabeth II bayan 'yar gajiriyar rashin lafiya da aka sanar ta yi a ranar Alhamis 8 ga watan Satumba, 2022.
Rahotanni daga majiyoyi sun shaida cewa, masarautar Ingila ta tashi bakin labarin jirkicewar lafiyar sarauniya, lamarin da yasa likitoci ke kai komo a kanta.
A wata sanarwar da masarautar ta Ingila ta fitar, an sanar da rasuwar sarauniyar da yammacin Alhamis.
Asali: Legit.ng