5G Ta Fara Aiki a Najeriya: MTN Ya Fara Gwaji A Birane 7
- Kamfanin MTN Nigeria ya kaddamar da fasahar 5G a wurare 190 a fadin Najeriya ranar Larabar nan
- Najeriya ta shiga jerin kasashe irinsu Afrika ta Kudu da Kenya inda tuni an fara amfani da fasahar 5G a Afrika
- Masu wayoyin Samsung da iPhone zasu jira sai lokacin da kamfoninsu suka inganta wayoyinsu
Kamfanin sadarwa na MTN ya kaddamar da gwajin fasahar 5G a Najeriya ranar Laraba kuma za'a fara da birane bakwai idan aka fara din-din-nin, kamfanin ya bayyanawa NGX, rahoton Premium Times.
MTN ya bayyana cewa an kafa hatsumuyoyin 5G guda 190 a fadin Najeriya musamman Legas da Abuja.
Wani rahoton BusinessDay yace an kaddamar da 5G a daidai ranar da hukumar sadarwa ta NCC tayi alkawarin za'a fara.
Jihohin da aka fara da su sun hada da Lagos, Port Harcourt, Ibadan, Abuja, Maiduguri, Kano da Owerri.
Rahotanni sun kara da cewa nan da watan Oktoba, ana kyautata zaton MTN zai kafa hatsumiyoyi 500 zuwa 600 a fadin Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Masu Amfani da Wayoyin Andriod Sun Shaida
A ranar Laraba, wasu wayoyi sun dauki 5G musamman masu amfani da Android.
Wasu wayoyin Samsung da iPhone zasu jira sai lokacin da kamfoninsu sun inganta fasahar.
Ana kyautata zaton cewa SamSung zai gyara wayoyinsa don amfanin yan Najeriya nan da watanni shida, yayinda masu IPhone zasu jira zuwa watan Oktoba.
Yayinda MTN ta fara nata, kamfanin Mafab Communications ya bukaci karin wa'adin watanni 5 kan ya fara amfani da nasa.
Kasashen Afrika masu 5G kawo yanzu
Najeriya ta shiga jerin kasashe irinsu Afrika ta Kusu da Kenya inda tuni an fara amfani da fasahar 5G a Afrika.
Kasar South Africa ta fara a wata Maris ta MTN da Vodacom.
Kasar Kenya kuwa ta fara a Afrillu ta kamfanin Safaricom.
Abin Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Sabuwar Fasahar 5G
A kan wannan gabar ne Legit.ng Hausa ta tuntunbi masanin fasahar sadarwa zamani da kwamfuta, Mallam Shehu Auwal mazaunin Kano don yin fashin baƙi game da batun.
Shehu Auwal ya bada amsa kamar haka:
"Toh shi 5G fasaha ce tamkar cigaba kan harkar sadarwa wato network, a baya ana amfani da wasu wayoyi ne da ake kira 'dial of connection' da ake latsa su kafin a samun damar hawa intanet.
"Daga baya kuma aka fara samun cigaban network irin gprs, sai aka samu edge, sannan aka samu 3G kana 4G ta fito."
Kamar yadda Mallam Auwal ya bayyana, fasahar 5G ya ɗara 4G wurin sauri sosai ta yadda likita daga ƙasar waje zai iya yin tiyata ba tare da ya iso Nigeria ba.
Hakan zai yiwu ne saboda za a sada shi ta intanet yana kallon duk abin da ke faruwa kuma ba za a samu tsaiko ba.
Asali: Legit.ng