Diraktan Hukuma Ya Mutu Bayan Fada Da Abokiyar Aiki a Katsina

Diraktan Hukuma Ya Mutu Bayan Fada Da Abokiyar Aiki a Katsina

  • Fada ya auku tsakanin abokan aiki biyu hukumar kare hakkin masiyi watau FCCPC kuma mutum daya ya mutu
  • Diraktan hukumar, Julius Haruna ya mutu ranar Laraba bayan sa'insa da Muibat Abdus- salam
  • Tuni dai an garzaya da matar komar yan sanda inda aka kaddamar da bincike kan wannan lamari

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Diraktan hukumar inganta tanafusi da kare hakkin masiyi watau Federal Competition and Consumer Protection Commission (FCCPC), shiyar jihar Katsina, Julius Haruna, ya mutu sakamakon fada da abokiyar aikinsa.

PM News ta ruwaito cewa Haruna ya mutu ne yayin fada da Muibat Abdusalam a Ofis ranar Laraba, 17 ga Agusta, 2022.

Jami'an yan sandan jihar Katsina sun tsare Muibat Abdusalam yayinda ake gudanar da bincike.

Katsina
Diraktan Hukuma Ya Mutu Bayan Fada Da Abokiyar Aiki a Katsina
Asali: UGC

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kara karanta wannan

Ana yi wa Hadimin Buhari Barazana da ICPC Saboda 'Cin' Albashi Bayan Ajiye Aiki

Hukumar FCCPC tayi tsokaci kan mutuwar Diraktan

Jawabi kan lamarin, Sakataren hukumar na kasa, Tam Tamunokonbia, a ranar Talata, 23 ga Agusta yace hukumar ta kafa na ta kwamitin bincike.

Tamunokonbia yace shugabannin hukumar sun bada umurnin dakatar da wasu manyan jami'an hukumar don tabbatar da an gudanar da bincike na gaskiya kan lamarin.

Yace:

"Hukumar yan sanda a Katsina na cigaba da gudanar da na ta binciken.Yanzu dai an garkame Misis AbdusSalamn a hannunta."
"Hukumar zata cigaba da bayyana duk labarin da abinda ya faru yayinda ake cigaba da gudanar da bincike."

Ya aika sakon ta'aziyya ga iyalan mamacin, abokansa da sauran abokan aikinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida

Tags: