Da dumi: Yan bindiga sun kashe Shehin Malami, Goni Asami, a jihar Yobe
- Labari da dumi-duminsa dake jihar Yobe na nuna cewa an kashe wani shehin Malami a jihar
- Har yanzu ana tattara wannan labari wanda ke cike da rudani
- Yayinda wasu ke zargin Sojoji da aika-aikan, wasu sun ce yan bindiga masu garkuwa da mutane ne
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Yobe - Wasu yan bindiga a ranar Asabar sun hallaka wani Shehin Malami mazauni jihar Yobe, Sheikh Goni Aisamu-Gashua a Jajimaji, hedkwatar karamar hukumar Karasua ta jihar.
Rahoto ya nuna cewa Malamin na hanyarsa ta zuwa Gashua ne daga jihar Kano yayinda suka biyoshi a baya kuma suka bindigesa.
ChannelsTV ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne misalin karfe 10 na safe a Jajimaji, mai nisan kilomita 10 da Gashua, mahaifar shugaban majalisar dattawan Najeriya.
Yan bindiga Sun Sako Kwamishanan Jihar Nasarawa
A wani labarin kuwa, yan bindiga masu garkuwa da mutane sun sako Kwamishanan labaran jihar Nasarawa, Hanarabul Mohammed Lawal Yakub, bayan kwashe kwanaki hudu hannunsu.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Kakakin hukumar yan sandan jihar, DSP Ramhan Nansel, ya bayyana hakan ne a hirar wayar tarho, rahoton Leadership.
Ya bayyana cewa Kwamishanan ya samu yancin ne ranar Juma'a, 19 ga Agusta, 2022.
Ya kara da cewa tuni an garzaya da kwamishanan asibiti domin duba lafiyarsa.
Asali: Legit.ng