Babu Nadamar Komai Saboda Tunbuke Ni, Kuma Ba Zan Yi Shiru Ba Inji Sanusi II

Babu Nadamar Komai Saboda Tunbuke Ni, Kuma Ba Zan Yi Shiru Ba Inji Sanusi II

  • Mai martaba Muhammadu Sanusi II yace sai dai ya godewa Allah a kan damar da ya samu a rayuwa
  • Khalifan Tijjaniya na Najeriya yake cewa idan har ya yi bakin-ciki, bai godewa baiwar Ubangiji ba
  • Tsohon Sarkin Kano ya bayyana cewa ba zai daina magana ba, zai cigaba da kare martabar kasar nan

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja – Mai martaba Malam Muhammadu Sanusi II ya bayyana cewa babu wata nadama da yake yi saboda ya rasa kujerar da yake kai na Sarkin Kano.

Daily Trust ta rahoto Muhammadu Sanusi II yana wannan jawabi a wani wasan kwaikwayo da aka shirya a game da tarihin rayuwarsa a birnin Abuja.

Basaraken ya yi magana game da aikin da ya yi a bankuna da masarautar gidan dabo da kuma zamansa shugaban mabiyar darikar Tijaniyah a duk Najeriya.

Kara karanta wannan

Sarkin Kano Sanusi: Duk da an tsige ni a sarauta, amma ba zan kame baki game da Najeriya ba

Tsohon Sarkin yace ya yi aiki a bankin United Bank for Africa da First Bank, bayan nan kuma har ya rike gwamnan babban bankin Najeriya watau CBN.

A watan Yunin 2014 ya zama Sarkin Kano, ya shafe tsawon shekaru shida a wannan kujera. Daga nan aka nada shi a matsayin jagora na darikar Tijaniya.

A cewar Sanusi II, ya yi butulci idan bai godewa Ubangiji da wadannan damammaki da ya ba shi ba, domin ba kowa ya samu baiwar da ya yi ta samu ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sanusi II
Khalifa Muhammadu Sanusi II Hoto: @MSII_dynasty / Majeeda Studio
Asali: Twitter

“Ba na tunani Ubangiji ya karbe wani abin daga gare ni. Saboda haka, ba n anadama. A shekarar bara na cika 61.
A shekarun nan na zama mai kula da fadawa cikin hadari na bankin United Bank of Africa da kuma First Bank.

Kara karanta wannan

Yajin ASUU: Yadda dalibin jami'a ya kama sana'ar siyar da shayi don yakar zaman kashe wando

Nayi gwamnan babban banki, Sarkin Kano, yanzu na zama Khalifah na tafiyar Tijaniyat a Najeriya.
Idan na yi fushi, ban gode ba. Mutum nawa suka samu daya daga cikin wannan dama da ni na samu."

- Muhammadu Sanusi II

Ba zan yi tsit ba

Jaridar ta rahoto Khalifa yana cewa iyayensa sun taimaka wajen gina Najeriya, yace mahaifinsa ne ya kafa NIA a 1960, yace zai cigaba da bada gudumuwarsa.

“A wuri na, babu wata nadama kuma zan cigaba da fadin ra’ayina. Zan cigaba da kare kasar nan."

- Muhammadu Sanusi II

Wasan kwaikwayo na Sanusi II

Farfesan wasan kwaikwayo, Ahmed Yerima ya bada umarni a wannan shiri mai suna “Emir Sanusi: Truth in Time’ da aka yi a kan tarihin Sanusi II.

Daily Post tace wanda ya shirya wasan kwaikwayon shi ne Joseph Edgar na kamfanin Somolu Productions domin duniya ta san gaskiyar tarihi.

Kara karanta wannan

Har gara 2015: Kasar nan na cikin ha’ula’i, ba a ga komai ba sai 2023 inji Sanusi II

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Tags: