Yan Ta'adda Sun Saki Sabon Bidiyon Yadda Suka Azabatar da Fasinjojin Jirgin Ƙasan Kaduna

Yan Ta'adda Sun Saki Sabon Bidiyon Yadda Suka Azabatar da Fasinjojin Jirgin Ƙasan Kaduna

  • 'Yan ta'addan da ke tsare da fasinjojin jirgin ƙasan Kaduna zuwa Abuja sun saki sabon bidiyo
  • Bidiyon ya nuna yadda suke azabtar da mutanen da ke hannun su da duka, kuma sun yi barazanar kai Najeriya ƙasa
  • Ɗaya daga cikin fasinjojin jirgin wanda ya yi magana a Bidiyon ya roki kasashen duniya su saka baki

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Kaduna - Ƙungiyar yan ta'adda waɗan da suka kai hari kan jirgin ƙasa da ke aiki tsakanin Abuja-Kaduna sun yi baranar tarwatsa Najeriya baki ɗaya.

A wani sabon Bidiyo da yan ta'adda suka sake, sun nuna yadda Fasinjojin jirgin kasa da ke tsare a hannun su ke rayuwa da yadda suke azabtar da su.

Harin jirgin ƙasa.
Yan Ta'adda Sun Saki Sabon Bidiyon Yadda Suka Azabatar da Fasinjojin Jirgin Ƙasan Kaduna Hoto: leadership
Asali: Twitter

A Bidiyon wanda jaridar Leadership ta rahoto, ɗaya daga cikin yan ta'adda ya ce wannan harin da suka kai har ya ta da hankalin kowa to bakomai bane a cikin hare-haren da suke shirin kai wa.

Kara karanta wannan

Hotuna da bidiyo: Alkawari ya cika, an daura auren 'Yaradua da Yacine kan sadaki sisin gwal 24

"Addinin Allah ya riga da ya ta shi kenan, kuma ku baku isa ku gama da Addinin Allah ba, saboda haka mu bayi ne na Allah, muna da tabbacin zai taimake mu."

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Kuma ku sani shirin mu ba wai Najeriya bane kawai duniya muka sa a gaba, ka da ku ga wanan aikin (harin jirgin ƙasa) ya ta da muku hankali, daga cikin ayyukan da muka sa a gaban mu wannan bai kai komai ba."

- inji ɗan ta'addan wanda ke rufe da fuskarsa.

Kalli Bidiyon anan:

Kasashen duniya su kawo mana ɗauki - Wani Fasinja

Da yake magana a cikin bidiyon, ɗaya daga cikin Fasinjojin da ke hannun yan ta'adda ya yi kira ga ƙasashen duniya su kawo musu ɗauki tun da gwamnatin Najeriya ta gaza.

"Ina kira ga ƙasashen duniya irin su Amurka, Saudiyya, Faransa da sauran su, su shigo lamarin nan, gwamnatin Najeriya ta hana yan uwan mu su karɓo mu, kuma mutanen nan ba su so mu wuce mako ɗaya ba, da an biya musu buƙatun su zasu sake mu."

Kara karanta wannan

Haɗin kan ƙasa da tsaron yan Najeriya zan sa a gaba, Buhari ya faɗi abinda zai yi bayan ya sauka mulki

A wani labarin kuma Shugaban ƙasa Buhari ya ce ko bayan ya bar mulki ba xai yi ƙasa a guiwa ba game da haɗin kai da tsaron yan Najeriya

Shugaban ƙasa Buhari ya ce ko bayan ya sauka daga mulki zai fi ba tsaro da haɗin kan ƙasa nuhimmanci a harkokinsa.

Buhari, wanda ya karɓi bakuncin masu ruwa da tsakin APC, ya gode musu bisa halin dattakon da suka nun a tafiyar da jam'iyya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262