Yanzu-yanzu: An damke Sanata Ekweremadu da matarsa kan yunkurin satar sashen jikin wani yaro
- An damke Sanata Ekweremadu da matarsa kan kokarin kai wani yaro kasar Birtaniya don satar sashensa
- Hukumar yan sandan birtaniya tace an garkamesu a kurkuku kuma zasu gurfana a kotu yau
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Hukumomi a kasar Birtaniya ta damke tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawan Najeriya, Ike Ekweremadu, da matarsa Beatrice kan laifin kai wani yaro kasar don cire wani sashen jikinsa.
Hukumar yan sandan kasar ta tabbatar da labarin cewa an garkamesu a kurkuku kuma za'a gurfanar da su a kotu ranar Alhamis bayan gudanar da bincike, rahoton Skynews.
Yan sandan sun kara da cewa an kaddamar da bincike ne bayan sanar da su wasu sun kawo dan wani kasar kuma hakan ya sabawa dokar bautar zamani na Birtaniya.
Jawabin yace:
"Beatrice Nwanneka Ekweremadu, 55 (10.9.66) na Najeriya ana tuhumarta da sufurin wani mutum da niyyar cire wani sashen jikinsa."
Bai Tsinana Mana Komai Ba: Matasa Da Mata Sun Huro Wuta A Karamar Hukuma, Sun Ce Dole A Tsige Ciyaman
"Ike Ekweremadu, 55 (10.9.66) na Najeriya ana tuhumarsa da sufurin wani mutum da niyyar cire wani sashen jikinsa."
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"An garkamesu kuma zasu gurfana gaban kotun Uxbridge yau."
"An kwace yaron hannunsu kuma ana kula da shi."
Asali: Legit.ng