An damke jami'in Soja zai gudu da bindiga AK47 da harsasai guda 30
- Jami'an Soji sun damke Soja yayinda yake kokarin guduwa da bindigar gwamnati da harsasai
- Sojan ya nemi hutu amma ya dauki bindigarsa ya tafi da shi kuma yaki dawowa bayan karewar hutunsa
- Wannan shine karo na hudu cikin shekarar nan da za'a kama soja da ake zargin yana aiki da yan ta'adda
Damaturu, Yobe - Jami'an hukumar Sojin Najeriya sun damke wani Soja mai suna, Tijjani Aliyu mai lamba 19NA/78/4786 kan laifin daukan makami ba bisa doka ba.
Sahara Reporters ta ruwaito cewa Sojan ya nemi hutu amma ya dauki bindigarsa ya tafi da shi kuma yaki dawowa bayan karewar hutunsa.
Wata majiya a gidan Soja ta bayyana cewa an damke Sojan ne makon da ya gabata a tashar Mota a Damaturu, jihar Yobe, da harsasan 7.62mm guda 30.
A jawabin da Soji suka saki,
"Jami'an rundunar Sect 2 Provost Gp on Op CHECKMATE sun damke 19NA/78/4786 LCpl Tijjani Aliyu na 199 bn dake NMP Sabon Gari a tashar motar Damaturu rike da bindiga AK 47 guda 1, magazin daya dauke da harsasai 7.62mm guda 30 boye cikin buhu."
"Bincike ya nuna cewa Sojan ya nemi hutu amma bai koma bariki ba bayan karewar wa'adin hutunsa. Bugu da kari, an gani cewa ya amshi bindigarsa da aka ajiye a dakin ajiyan makamai dake 231 bataliya Biu kafin tafiya hutu, wanda hakan nuna niyyarsa. An garkameshi don bincike."
Kano: Ƴan Sanda Sun Kama Sojan Bogi, Zailani-Ibrahim Da Ya Ƙware Wurin Tatsar Masu Keke Napep
A wani labarin kuwa, rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta samu nasarar damkar sojan bogi wanda ya kware wurin damfarar masu Napep, The Nation ta ruwaito.
Jami’in hulda da jama’an rundunar, DSP Abdullahi Kiyawa ne ya tabbatar da kamen a wata takarda wacce ya ba manema labarai ranar Talata a Kano.
A cewarsa, wanda ake zargin, Abubakar Zailani-Ibrahim, mai shekaru 27 ya gabatar wa da ‘yan sandan ofishin Rijiyar Zaki kansa a matsayin soja kuma ya je da wani mai Napep.
Asali: Legit.ng