Ziyarar Buhari: Kada wanda ya fita waje yau da gobe, yan bindigan IPOB sun gargadi mutan yankin Igbo
1 - tsawon mintuna
- Yan bindigan da suka addabi yankin kabilar Ibo sun saki sabon umurni ga al'ummar yankin bisa ziyarar shugaba Buhari
- Yan ta'addan na IPOB sun ce kada wanda ya fito waje tarbar Buhari, kuma wanda yayi za'a fuskanci hukunci
- Shugaba Buhari ya kai ziyarar kwanaki biyu jihar Ebonyi don kaddamar da wasu ayyukan gwamna Dave Umahi
Wasu yan bindiga masu tada zaune tsaye a yankin kudu maso gabas sun bada umurnin kada kowa ya fita waje ranakun 5 da 6 ga Mayu, 2022 sakamakon ziyarar kwana biyu da shugaba Buhari ya kai jihar Ebonyi.
Leadership tace a cewar wata majiya daga gidan Soja, yan bindigan sun mamaye wasu garuruwa da jihohin Abia, Imo da Anambra ranar Laraba kuma sun yi barazanar hallaka duk wanda ya saba wannan umurni.
A cewar majiyar:
"An ga yan bindiga na harbe-harbe a wasu unguwannin Aba dake Abia, Imo da Anambra suna sanar da cewa kada wanda ya fito waje ranar Alhamis da Juma'a lokacin Shugaba Buhari zai ziyarci jihar Ebonyi, kuma wajibi ne abi umurnin a dukkan jihohin Kudu maso Gabas."
Yan bindigan sun yi kira ga shugaba Buhari ya yi gaggawan sakin shugaban kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Asali: Legit.ng
Tags: