Sabon Gwamnan Anambra ya ba Buhari shawarar abin da ya kamata ayi wa Nnamdi Kanu

Sabon Gwamnan Anambra ya ba Buhari shawarar abin da ya kamata ayi wa Nnamdi Kanu

  • Sabon gwamnan Anambra, Farfesa Charles Chukwuma Soludo ya na kokarin kawo zaman lafiya
  • Charles Chukwuma Soludo ya bude kofar sulhu da ‘yan ta’addan da su ka addabi kudu maso gabas
  • Gwamna ya na ganin bai dace cigaba da rike Nnamdi Kanu ba tare da kotu ta yi masa hukunci ba

Anambra - Gwamnan jihar Anambra, Charles Chukwuma Soludo ya yi alkawarin zai yi kokari wajen ganin an shawo kan matsalar tsaro a Kudu maso gabas.

Jaridar Premium Times ta rahoto Mai girma gwamnan ya na wannan jawabi a farkon makon nan, ya ce zai sa gwamnatin tarayya tayi sulhu da tsagerun IPOB.

Farfesa Charles Chukwuma Soludo ya na ganin idan aka fito da jagoran IPOB, Nnamdi Kanu, za a samu saukin matsalar tsaro da ake fama da ita yau a jihohin Ibo.

Kara karanta wannan

Mai magana da yawun bakin Jam’iyyar PDP ya ce Gwamnan APC ya nemi ya kashe shi

Gwamna Charles Chukwuma Soludo ya yi wannan jawabi ne a wajen wani taro da ya shirya a garin Awka domin kawo karshen halin dar-dar a jihar Anambra.

An yi addu'o'i na musamman a coci

Rahoton ya nuna cewa gwamnan ya amince da 4 ga watan Afrilu a matsayin ranar addu’o’i a coci kamar yadda sarakunan gargajiyan jihar su ka bada shawara.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A taron ne ya kawo batun Nnamdi Kanu wanda har yanzu yake tsare, ba tare da an yanke masa hukunci, ya ce akwai bukatar gwamnatin tarayya ta fito da shi.

Sabon Gwamnan Anambra
Charles Chukwuma Soludo a gidan gyaran hali Hoto: @CCSoludo
Asali: Twitter

Za a yi wa 'Yan bindiga afuwa a Anambra

Soludo ya yi alkawari gwamnatinsa za ta bude cibiyoyi domin kula da tubabbun ‘yan bindiga, muddin su ka ajiye makamansu, su ka daina tada zaune-tsaye.

Sabon gwamnan ya na ganin akwai bukatar a bi hanyar lalama domin a kawo zaman lafiya. Daga cikin yadda za a cin ma hakan, shi ne a fito da shugaban na IPOB.

Kara karanta wannan

Neman kujerar Shugaban kasa ya barka Atiku, Saraki da ‘Yan takarar PDP, kai ya rabu 3

Matsayar Mai martaba Alfred Achebe

Mai martaba Sarkin Onitsha, Alfred Achebe ya karanto matsayar da aka dauka a madadin gwamnatin Anambra, ya ce sun nemi su zauna da shugaban kasa.

Achebe wanda ya yi magana da yawun fastoci, sarakunan gargajiya da kuma gwamnatin jihar Anambra ya ce har yanzu ba su ji daga fadar shugaban kasar ba.

Haka ya kamata gwamnati ta yi - Ringim

Abdulhaleem Ishaq Ringim wanda ya saba tofa albarkacin bakinsa a kan abubuwan da suka shafi kasa, ya yaba da matakin da Farfesa Soludo ya dauka a shafinsa.

Malam Ringim ya ce akwai bukatar a bar kofar sulhu da ‘yan ta’adda a bude. Sannan kuma ana bukatar malamai da sarakunan gargajiya wajen kawo zaman lafiya.

A ra'ayinsa, ba zai yiwu a yi galaba da karfin bindiga ba, don haka dole a bi ta hanya irin ta lalama.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng