Kotu ta sa ranar da za a saurari shari’ar damka Abba Kyari ga hukumomin kasar Amurka
- A yau babban kotun tarayya mai zama a garin Abuja ya saurari karar da aka kai DCP Abba Kyari
- Incorporated Trustees of Northern Peace Foundation ta na so a hana a mika Kyari ga Amurkawa
- FBI ta na zargin jami’in ‘dan sandan ya na da alaka da wani wanda ake zargi da laifin damfarar jama'a
Abuja - Babban kotun tarayya da ke zama a garin Abuja, ya daga wata kara da ake yi da babban jami’in ‘dan sandan nan da aka dakatar, DCP Abba Kyari.
Vanguard ta fitar da rahoto cewa a ranar Litinin aka zauna kan karar da aka shigar domin hana gwamnatin tarayya mika Abba Kyari ga hukumomin Amurka.
Alkali ya daga wannan shari’a zuwa ranar 4 ga watan Yuli 2022 domin a cigaba da zama a kotu.
Wadanda aka shigar a wannan shari’a mai lamba ta FHC/ABJ/CS/854/2021 sun hada da rundunar ‘yan sandan Najeriya da Ministan shari’a, Abubakar Malami.
Rahoton ya ce Mai shari’a Donatus Okorowo ya daga wannan zama ne bayan duka bangarorin sun gagara halartar zaman kotun da aka yi yau a garin na Abuja.
Babu wanda ya je kotu a yau
A lokacin da Donatus Okorowo ya kira wadanda suka shigar da kara da wadanda ake tuhuma a kotu, babu lauyan kowane bangare da ya samu halartar zaman.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Okorowo wanda a baya ya yi barazanar yin fatali da wannan kara daga gabansa saboda yadda lauyoyin bangarorin ke wasa da shari’ar, ya sake bada wata dama.
Mai shari’an ya bukaci a sanar da wakilan gwamnati da na masu shigar da kara game da ranar da aka sa domin gudun irin hakan ta sake faruwa idan an zo zama.
A farkon watan Yulin shekarar nan za a koma kotu domin a karkare wannan shari’a. Hakan ya na nufin nan da kwanaki kimanin 71 ake sa ran za a hallara a kotu.
Za a kai Kyari gaban FBI?
The Cable ta ce wata kungiya mai suna Incorporated Trustees of Northern Peace Foundation ce ta shigar da wannan kara domin hana a mika Kyari ga jami’an FBI.
Kwanaki aka ji Ministan Shari'a na kasa, Abba Kyari ya yi tsokaci kan inda aka kwana kan lamarin hazikin dan sanda, Abba Kyari da yanzu ya shiga hannu.
Abubakar Malami SAN ya bayyana cewa Gwamnatin Amurka da ta Najeriya su na tattaunawa kan yiwuwar mika jami'in dan sandan saboda zargin almundahana.
Asali: Legit.ng