Mayakan ISWAP 7,000 sun ajiye makamai tare da mika wuya a mako 1, Rundunar soji
- A kalla mayakan ISWAP guda 7,000 ne suka mika wuya ga rundunar sojin Najeriya a satin da ya gabata a jihar Borno
- Kwamandan tawagar Operation Hadin Kai na hukumar hadin gwuiwa ta arewa maso gabas ne ya bayyana hakan a Maiduguri.
- Musa ya labarta yadda dakarun sojojin suka kai wa mayakan ISWAP da Boko Haram samame a yankin arewa maso gabas, inda suke cigaba da samun nasarori a kansu
A kalla mayakan ISWAP guda 7,000 ne suka mika wuya ga rundunar sojin Najeriya a satin da ya gabata, Daily Nigerian ta ruwaito.
Christopher Musa, Kwamandan tawagar Operation Hadin Kai ( OPHK), na hukumar hadin gwuiwa ta arewa maso gabas ne ya bayyana hakan a ranar Laraba yayin tattaunawa da kamfanin dillancin labaran Najeriya a Maiduguri.
Sojoji na cigaba da samun nasara kan yan taadda
Musa ya bayyana yadda dakarun sojojin suka kai wa mayakan ISWAP da Boko Haram samame a yankin arewa maso gabas, inda suke cigaba da samun nasarori a kansu.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A cewarsa: "Wannan alamar na nuna yadda dubbannin yan ta'addan da suka hada da yan fashi da makami, da marasa makami, mayaka a kasa tare da iyalansu, na cigaba da yada makamansu a sasanni daban-daban na jihar Borno don rungumar zaman lafiya."
Musa ya bayyana yadda ake sa ran rundunar sojin Najeriya da sauran jami'an tsaro za su cigaba da sa ido a kan yan ta'addan da iyalansu don gudun sake komawa ruwa.
Kwamandan tawagar ya bayyana yadda sojin Najeriya da sauran jami'an tsaro za su cigaba da kokari wajen tabbatar da kawo karshen ta'addancin Boko Haram ba tare da jinkiri ba.
Jiragen Super Tucano sun yi lugude a maboyar ISWAP, Sani Shuwaram ya shura lahira, an nada sabon shugaba
Jami'an tsaro sun ce, tuni yan ta'adda guda 30,000 da iyalansu suka mika wuya ga dakarun sojin Najeriya a watanni tara da suka gabata.
An kaddamar da OPHK a ranar 30 ga watan Afirilu, 2021, Daily Nigerian ta ruwaito.
Rundunar sojin kasan Najeriya ta canza suna atisayen Lafiya dole, wanda shi ne taken atisayan nata na yaki da Boko Haram, zuwa Atisayen Hadin Kai.
Borno: An halaka mayakan ISWAP, sojoji sun dakile harin miyagu a sansanin soji
A wani labari na daban, wasu majiyoyin soji sun shaidawa jaridar TheCable cewa, dakarun Operation Hadin Kai sun kashe mayakan kungiyar IS da ke yammacin Afirka (ISWAP) da dama a Borno.
An ce maharan sun kaddamar da harin ne a sansanin sojojin da ke Doron Baga a karamar hukumar Kukawa da sanyin safiyar Asabar.
Majiyoyi sun ce mayakan dauke da gurneti da manyan motocin bindigu 5 ba su samu galaba a kan sojojin.
Asali: Legit.ng