Ido zai raina fata yayin da Shugaban kasa ya ce a hukunta wanda suka jawo wahalar fetur
- Muhammadu Buhari ya amince a hukunta duk wadanda suka jawo wahalar man fetur a Najeriya
- Shigo da fetur wanda yake kunshe da tulin sinadarin Methanol ya taimaka wajen kawo wahalar mai
- Shugaban kasa ya bada umarnin hakan kafin ya bar Najeriya zuwa kasar Birtaniya kwanakin baya
Abuja - Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yarda a dauki tsattsauran mataki a kan wadanda suka shigo da man fetur din da ba a amfani da irinsa.
Jaridar The Cable ta fitar da rahoto a karshen makon da ya gabata, da ya nuna shugaban kasa ya yarda a hukunta wadanda aka samu da laifin shigo da man.
Idan za a tuna, a watan Fubrairu Legit.ng Hausa ta kawo rahoto cewa gwamnatin tarayya ta sha alwashin hukunta duk masu hannu wajen shigo da wannan fetur.
Hakan na zuwa ne bayan hukumar Nigerian Midstream and Downstream Petroleum Regulatory Authority (NMDPRA) ta tabbatar da samun fetur mai Methanol.
Rahoton ya nuna an dauki wannan matsaya ne a wajen majalisar zartarwa ta kasa watau FEC wanda Farfesa Yemi Osinbajo ya jagoranta a makon da ya wuce.
An fito da wasu tsare-tsare
Majiyar ta ce wahalar man fetur da aka saba fama da shi ya ragu sosai a gwamnatin nan, kafin aukuwar wannan lamari da ya fusata Mai girma shugaban kasa.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Mai girma Muhammadu Buhari ya kawo tsarin da za a bi domin a kawo karshen wahalar man fetur da ake fama da shi a halin yanzu a kusan duk jihohin kasar nan.
Daga cikin dabarun da aka kawo shi ne a hukunta duk wanda yake da hannu wajen barin wannan fetur mai yawan Methanol ya shigo Najeriya ba tare da an duba ba.
Abubuwa sun lafa?
Jaridar ta ce kafin Buhari ya wuce kasar waje, sai da ya amince a hukunta masu laifin saboda ganin ba a sake samun faruwar irin wannan kuskure a nan gaba ba.
A sakamakon wannan umarni da shugaba Buhari ya bada ne aka ga fetur ya fara wadata a gidajen mai. NNPC sun sa dole a rika saida fetur babu dare-babu rana.
Sannan darektan DSS na kasa, Yusuf Bichi, ya taimakawa shugaban NNPC, Mele Kyari wajen ganin ana jigilar motocin mai zuwa garuruwa domin a samu sauki.
Ana raba litocin fetur
Idan har ba ku manta ba, kun ji labari cewa a makon karshe na watan Fubrairu, NNPC sun ce sun fitar da litoci fiye da miliyan 380 na man fetur domin rage wahalar mai.
Duk da ikirarin da NNPC ya ke yi na cewa tana fitar da miliyoyin litocin man fetur, har yanzu ana fama da matsanancin wahalar man jirgin sama da kuma bakin man dizil.
Asali: Legit.ng