Labari da dumi-dumi: DCP Abba Kyari da mutum 6 sun bayyana a kotu, za a gurfanar da su
- Babban jami’in ‘dan sanda DCP Abba Kyari ya iso babban kotun tarayya da ke zama a garin Abuja
- Hukumar NDLEA za tayi shari’a da Abba Kyari da wasu mutum shida kan zargin badakalar kwayoyi
- Dakaru sun yi wa wadannan mutane rakiya daga inda suke tsare zuwa kotun mai zama a Abuja
Abuja - Abba Kyari da wasu mutane shida da ake zargi da hannu wajen badakalar miyagun kwayoyi sun bayyana a harabar babban kotun tarayya a Abuja.
The Nation ta kawo rahoto a safiyar Litinin, 7 ga watan Maris 2022 cewa DCP Abba Kyari sun shigo kotu, ana sauraron a gurfanar da su a gaban Alkali.
Jami’an hukumar NDLEA mai yaki da masu safarar miyagun kwayoyi ne suka kai Kyari da ragowar ‘yan sanda da mutane biyu da ake zargi zuwa kotu.
Dakarun NDLEA biyu da suka jagoranci wadannan mutane da ake tuhuma, su na dauke da makamai.
Jaridar ta ce an ga Abba Kyari sanye da tufafi mai launin tsanwa a harabar kotun. Jami’in ‘dan sandan ya hallara ne a cikin wata katuwar motar gwamnati.
Ragowar mutane hudun da za ayi shari’a da su a zaman yau sun iso ne a cikin wasu motocin Hilux. A halin yanzu duk su na jiran zuwan malaman shari’a.
‘Dan sandan da aka dakatar daga aiki da sauran wadanda suke tare da shi su na zaune, su na jiran isowar Alkalin da zai saurari shari’arsu da hukumar NDLEA.
DCP Kyari za su amsa zargin aikata laifuffuka takwas da suka shafi harkar miyagun kwayoyi. NDLEA tana zargin su na da hannu wajen shigo da hodar iblis.
Bidiyon Kyari a kotu
Premium Times ta fitar da wani bidiyo inda aka ga Kyari da sauran takwarorinsa sun iso kotun da za ayi zama. Za a iya ganin Kyari ya rufe fuskarsa da amawali.
Daga baya an hangi su Kyari su na gaisawa da sauran wadanda ake zargi yayin da ya tankwasa kafa a kan kujera, su na sauraron isowar sauran jama’a a kotu.
Rana ba ta karya
Dazu ku ji Hukumar NDLEA za ta yi shari’a da su Abba Kyari a kan zargin aikata laifuffuka takwas da suka shafi safarar kwayoyi a gaban Mai shari’a Emeka Nwite.
Sauran wadanda za su kare kansu a wannan shari’a su ne; Ubia, Bawa James, Simon Agirigba da John Nuhu. Sai Chibunna Patrick Umeibe da Emeka Ezenwanne.
Asali: Legit.ng