Sai Miji Na Ya Lakaɗa Min Baƙin-Duka Sannan Yake Kwanciya Da Ni, Mata Ta Nemi Saki a Kotu
- Wata mata, Olamide Lawal ta bukaci kotun gargajiya mai daraja ta daya da ke Ibadan ta raba aurenta da mijin ta saboda shaye-shayen shi
- Ta zargi mijin ta, Saheed da dukan ta tare da lalata da matan banza, wanda daga nan alkalin kotun, S. M. Akintayo ya amince ya raba su
- Har ila yau, alkalin ya bukaci matar ta rike yaran saboda zargin miyagun halayen mijin za su iya tasiri ga yaran matsawar aka bar su a hannun shi
Jihar Oyo - Wata kotun gargajiya mai daraja ta farko a Ibadan ta raba auren wata mata, Olamide Lawal bisa halayyar mijin ta na shaye-shaye da fasikanci, Daily Nigerian ta ruwaito.
A korafin da Ma Lawal ta yi, ta zargi mijinta, Saheed da dukan ta tare da lalata da matan banza.
Yayin yanke hukunci, alkalin kotun, S. M. Akintayo ya ce kotun ta raba auren ne saboda Saheed ya ki zaman lafiya da kuma bin dokar da hukuma ta gindaya masa.
Alkalin ya ba matar damar rike yaran ta guda 3
Kamar yadda Daily Nigerian ta bayyana, alkalin ya ce:
“Wanda ake kara ya nuna cewa miyagun halayen sa zasu iya tasiri akan yara ukun da suke da su matsawar aka kyale su a hannun shi.
“Don haka an ba mai kara damar rike yaran saboda gudun Saheed ya gurbata tarbiyyar yaran. Amma an ba shi damar zuwa ganin yaran a duk Asabar din ko wanne karshen wata.
“Sannan kotu ta hana shi zuwa gida da kuma shagon tsohuwar matar tasa.”
Mr Akintayo ya umarci Saheed da ya dinga kai wa magatakardar kotun N15,000 a matsayin kudin abincin yaran.
Dama tun farko a korafin Ms Olamide ta sanar da kotu cewa mijin ta yana cin zarafin ta kafin ya kwanta da ita inda tace hakan yana matukar ci mata tuwo a kwarya.
Ta bukaci kotu ta raba auren su don ta gaji da hakuri da miyagun halayen sa.
Saheed bai so aka raba auren su ba
A cewarta:
“Yana duka na kafin ya kwanta da ni. Yana shaye-shaye kuma bai damu da yaransa ba. Bayan na kai kararsa ofishin ‘yan sanda an yi yarjejeniya da shi akan cewa ba zai sake duka na ba.”
Ta ci gaba da shaida yadda ya ci gaba da dukan ta.
Saheed wanda tela ne ya nuna rashin amincewarsa akan sakin. Ya ce ya sauya halayen sa kuma ya daina dukan ta. Ya kuma yi alkawarin cewa ya daina shaye-shaye.
Asali: Legit.ng