Gwamnatin Kaduna ta ankarar da al’umma, ta ce ayi hattara da boyayyen shirin ‘Yan ta’adda
- Gwamnatin jihar Kaduna ta ja-kunnen jama’a a kan yiwuwar ‘yan ta’adda na shuka bama-bamai
- Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida ya fitar da jawabi yana gargadin mutanen jihar Kaduna
- Samuel Aruwan ya ce a tuntubi wadannan lambobi: 09034000060 da 08170189999 idan da matsala
Kaduna - Gwamnatin jihar Kaduna ta gargadi mutane da cewa su sa ido domin babu mamaki ‘yan ta’adda sun birne bama-bamai a wasu yankunan jihar.
Legit.ng Hausa ta na da labari cewa wannan sanarwar ta fito ne daga bakin ma’aikatar tsaro da kuma harkokin cikin gida na jihar Kaduna a ranar Litinin.
Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na Kaduna, Samuel Aruwan ya ce suna tsoron ‘yan ta’addda na kokarin dasa bam a inda jama’a su ke taruwa.
Daga cikin inda ake ganin za a iya kai wa hari akwai makarantu, asibitoci, otel, gidajen rawa da wasanni, wurin cin abinci, hanyoyi da majami’an ibada.
Kamar yadda sanarwar ta bayyana, jami’an tsaro su na bakin kokari domin kare rai da dukiyar jama'a. Aruwan ya fitar da jawabin nan a shafin Facebook.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Cikakken jawabin da aka fitar
“Gwamnatin jihar Kaduna tana jan-kunne na musamman ga mutanen da ke jihar domin ankarar da su a kan barazanar shuka bam-bamai a wuraren da jama’a suke taruwa.”
“Hakan ya biyo bayan binciken da jami’an tsaro suka yi, da yiwuwar ‘yan ta’adda na kai wa al’ummar gari hari ta hanyar dasa bam a boye a makarantu, asibotoci, otel, gidajen rawa da wuraren shan lemu, wuraren wasanni, dakunan cin abinci, manyan tituna da wuraren ibada.”
“Jami’an tsaro su na kokari domin tabbatar da cewa wannan ta’adi bai auka a kan wani mazaunin jihar ba.”
“Saboda haka ana kira ga mazauna da su zama idanunsu a bude game da wannan barazana, su sa ido a kan mutanen da ba a yarda da su ba da kayan da ake jibgewa a wuraren da babu kowa.”
“Ana bada shawarar a kara lura da kyau, a rika yawan bibiyar wurare bini-bini.” - Samuel Aruwan.
A karshe gwamnati ta bada lambobin wayar da za a tuntubi jami’ai idan an ci karo da wani abu da ake zargi. Lambobin wayoyin su ne 09034000060 da 08170189999.
Tashin bam a Kabala
A farkon makon nan ne jami’an tsaro su ka tabbatar da fashewar wani bam a yankin Kabala West da ke cikin garin Kaduna. An ci sa'a babu wani wanda ya mutu.
'Yan sanda sun fitar da sanarwa ta musamman, sun tabbatar da aukuwar wannan lamari. Mohammed Jalige ya yi jawabi a madadin rundunar ‘yan sanda.
Asali: Legit.ng