Kungiyar ASUU za ta yi zaman farko da Gwamnatin Tarayya mako 1 da fara yin yajin-aiki
- Shugabannin kungiyar malaman jami’a na kasa su na shirin haduwa da Ministan kwadago yau
- Farfesa Emmanuel Osodeke ya tabbatar da cewa za su yi wani zama tare da Chris Ngige a Abuja
- Jami’in ma’aikatar kwadago ta kasa, Charles Akpan ya ce da karfe 1:00 na rana za a shiga taron
Abuja - A ranar Talata, 22 ga watan Fubrairu 2022 ne shugabannin kungiyar malaman jami’a na ASUU za su yi zama da wakilan gwamnatin tarayya.
Jaridar Premium Times ta fitar da rahoto a ranar Litinin, ta ce za ayi wannan zama ne da nufin shawo kan sabanin da ke tsakanin duk bangarorin biyu.
Shugaban kungiyar ASUU na kasa baki daya, Farfesa Emmanuel Osodeke ya tabbatarwa manema labarai cewa za su zauna da bangaren gwamnatin kasar.
Iyakar abin da Farfesa Emmanuel Osodeke ya shaidawa manema labarai a waya shi ne za ayi wannan zama, ba tare da ya bada wani karin bayani ba.
Wata majiya ta bayyana cewa Ministan kwadago na kasa, Chris Ngige ne ya kira taron a matsayinsa na mai sasanta gwamnati da ma’aikatanta.
Za dai mu je ne kawai - Majiya
Sai dai malaman jami’ar ba su tunanin zaman na yau zai iya haifar da wani ‘da mai ido, amma duk da haka za su halarta domin gudun a daura masu laifi.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
“Mun riga mun samu gayyata, abin da zan fada maku kenan. Ba na tunanin wani zaman kirki ne, amma za mu je saboda tsoron bata mana suna.”
Minista ya nemi a zauna
Jaridar Vanguard ta ce Mai girma Ministan kwadago da samar da aikin yi na kasa, Dr. Chris Ngige ne ya aikawa shugabannin ASUU goron gayyata domin a zauna.
Mai magana da yawun bakin ma’aikatar tarayyar, Charles Akpan ya shaidawa jaridar wannan. A cewarsa za a soma wannan taro ne da karfe 1:00 na rana a ofishin na su.
“Minista zai hadu da ASUU a ranar Talata da karfe 1:00 na rana. Za ayi zaman a ofishin ma’aikata.”
- Charles Akpan
Babu taron NEC
A gefe guda, shugaban ASUU na shiyyar Legas, Laja Odukoya ya musanya rahotannin da ke yawo na cewa majalisar koli ta NEC za ta yi wani taro kwana nan.
Laja Odukoya ya ce babu gaskiya a wannan rade-radi, ya ce NEC ba ta kira wani taro a Legas ba.
A ranar Lahadi, 19 ga watan Disamba, 2021, ASUU tayi wani zama a birnin tarayya Abuja, inda aka yanke shawarar a janye yajin-aikin da aka yi shekara ana yi.
Watanni 13 da yin wannan sai aka ji ASUU ta sake komawa yajin-aiki. Bugu da kari, kungiyar COEASU ta makarantun horas da malamai na tunanin ta bi ASUU.
Asali: Legit.ng