Babu ruwanmu: Ba mu shigo da man fetur maras kyau ba – MRS sun karyata bidiyo

Babu ruwanmu: Ba mu shigo da man fetur maras kyau ba – MRS sun karyata bidiyo

  • A halin yanzu an samu rubabben man fetur wanda yake yawo da zai iya lalata abin hawa da na’urori
  • Kamfanin MRS Oil Nigeria Plc ya ce sam bai da hannu wajen shigo da wannan bara-gurbin fetur
  • A wata sanarwa da ta fito daga kamfanin, an ji cewa sun yi kokarin hana wannan mai ya zagaya

Abuja - Kamfanin MRS Oil Nigeria Plc da ke shigo da man fetur ya ce ba shi da laifin shigowa da raba bara-gurbin man fetur da ya zagaye kasar nan.

Ana zargin cewa MRS Oil Nigeria Plc na cikin wadanda suke da alhakin shigo da wannan mai. The Cable ta rahoto kamfanin ya na musanya hakan.

A wani bidiyo da yake yawo a kafafen sadarwa na zamani, an ga wani ma’aikaci dauke da rigar gidan man MRS ya na zuba rubabben man fetur a gora.

Kara karanta wannan

Shugaban NNPC ya bayyana wadanda suka shigo da rubabben fetur daga kasar waje

A cewar MRS Oil Nigeria Plc, wannan zargi da ake yi masu sharri ne kurum da kuma kage.

Kamfanin na MRS Oil Nigeria Plc ya bayyana cewa ba ya shigo da premium motor spirit ko PMS wanda mutane su ka fi sani da man fetur a Najeriya.

Jaridar ta rahoto kamfanin ya na cewa NNPC kadai ke da nauyin dakon man fetur cikin kasar nan a dalilin tsarin tallafin man fetur da gwamnati ta kawo.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Man fetur
Ana shan man fetur Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

NNPC ta hannun kamfanin Duke Oil ya saye man fetur daga wajen kamfanin ketare na Litasco, ya shigo da shi da motar motor tanker (MT) Nord Gainer kwanaki.

MRS ya ce an sauke wannan man fetur a tashar ruwa na Apapa a karshen Junairu, aka rabawa ‘yan kasuwa. Su kuma ‘yan kasuwar suka rabawa gidajen mai.

Kara karanta wannan

Gurbataccen man Fetur: FG na iya mayar da mai ga masu kawo shi, abun ya shafi lita miliyan 100 - Yan kasuwa

A cewar MRS, sun samu metric ton 5, 000 na wannan rubabben fetur a watan Junairun 2022, sun gane cewa man ya gurbata, sai su ka ki fito da shi a kasuwa.

“Bincike ya nuna man PMS da MT Nord Ganier ya sauke yana dauke da 20% na methanol alhali a Najeriya ba a halasta amfani da wannan sinadari ba.”
“A matsayinmu na kamfani, mun san ba a aiki da alcohol/ethanol. Nan take mu ka sanar da NNPC, NMDPRA da MOMAN, aka tabbatar mana da haka.”

- MRS Oil Nigeria Plc

Zuwa lokacin da aka fitar da wannan rahoto, kamfanin na MRS ya ce yana da lita 350, 000 na wannan rubabben mai da ake jiran a maidawa NNPC da NMDPRA.

Shugaban NNPC ya yi magana

A jiya Malam Mele Kolo Kyari ya ce a karshen watan Junairun 2022 ne jami’an NNPC suka fahimci wasu sun yi dakon fetur maras kyau cikin Najeriya.

Kara karanta wannan

Mun shiga uku: Tsadar man fetur ya sa 'yan Najeriya kuka, sunyi zazzafan martani

Shugaban kamfanin na NNPC ya jero sunayen kamfanonin da suka shigo da wannan mai daga kasar Belgium ba tare da an ankara ba, daga ciki har da MRS.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng