Kungiyar Dattawan Yarabawa: Malami ya fito ya fada wa ‘yan Najeriya dokar da Igboho ya karya

Kungiyar Dattawan Yarabawa: Malami ya fito ya fada wa ‘yan Najeriya dokar da Igboho ya karya

  • Kunle Olajide, sakatare janar na kungiyar dattawan Yarabawa ya bukaci antoni janar na kasa, Abubakar Malami, ya sanar da laifukan da Sunday Igboho ya yi
  • A cewarsa hakan ne zai ba ‘yan Najeriya damar fahimtar abinda gwamnatin tarayya take nema a shari’ar da za ta yi da Igboho
  • Dama a ranar Talata Malami ya ce gwamnatin tarayya za ta iya gurfanar da dan tawayen da zarar hukumar jamhuriyar Benin ta sako shi

Sakatare janar na kungiyar dattawan Yarabawa, Kunle Olajide ya bukaci antoni janar na kasa, Abubakar Malami ya zayyana wa ‘yan Najeriya laifukan da Sunday Adeyemo, mai rajin kafa kasar yarabawa, wanda aka fi sani da Sunday Igboho, ya aikata, The Cable ta ruwaito.

A cewarsa, hakan ne zai ba ‘yan Najeriya damar gane abinda gwamnatin tarayya take bukata a shari’ar da take shirin yi da Igboho.

Kara karanta wannan

Malami: Akwai yuwuwar FG ta hukunta Igboho a Najeriya bayan Cotonou ta sake shi

Kungiyar Dattawan Yarabawa: Malami ya fito ya fada wa ‘yan Najeriya dokar da Igboho ya karya
Malami ya fada wa ‘yan Najeriya dokar da Igboho ya karya, Kungiyar Dattawan Yarabawa. Hoto: The Cable
Source: Twitter

Yayin da ya amince da cewa za a iya samun mafita a siyasance, Olajide ya ce ta yuwu shawarar da Malami yake ganin zata iya bullewa ta bambanta da ta wurin Buhari.

A ranar Talata, Malami ya ce gwamnatin tarayya zata iya gurfanar da dan tawayen bayan hukumar jamhuriyar Benin ta sake shi.

Yayin mayar da martani dangane da furucin Malami, Olajide ya sanar da The Cable cewar zai zama shari’a biyu kenan idan har gwamnati ta gurfanar da Igboho bayan shari’ar da ya yi a kasar waje.

Olajide ya ce ya kamata a yi dubi akan yadda jami’an tsaro suka halaka wasu mutan gidan Igboho

Olajide ya ce a yi dubi da yadda jami’an tsaron gwamnatin tarayya suka afka gidan Igboho wanda har aka halaka wasu daga cikin mazauna gidan, ya bar Najeriya amma duk da haka rayuwarsa tana cikin hadari.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Jamhuriyar Benin ta yanke sake tsare Sunday Igboho na tsawon watanni

Kamar yadda Olajide ya ce:

“Zai zama shari’a har biyu kenan. Wacce doka Igboho ya karya? Ya kamata Malami ya yi bayani dalla-dalla yadda wadanda basu san kan shari’a ba zasu gane.
“Maganar da ya yi ba ta fadada ba musamman bayan ganin yadda aka afka har gidan Igboho aka halaka mutane cikin dare.
“A bayyane yake, rayuwar Igboho ake farauta. Don haka wacce doka Igboho ya karya bayan an afka gidan sa? Malami ya yi wa ‘yan Najeriya bayani.”

Ya ce akwai yiwuwar a samu mafita a siyasance

Yayin da ya amince da cewa za a iya samun mafita a siyasance, Olajide ya ce ta yuwu shawarar da Malami yake ganin za ta iya bullewa ta bambanta da ta wurin Buhari.

A cewarsa:

“Mafitar da ya fadi a siyasance ta danganta da abinda ke zuciyar shugaban kasa.
“Ta yiwu shugaban kasa ya yi dubi wanda ya bambanta da shawarar sa. Shi ya fi kowa sanin mafitar siyasar da ya yi magana akai. Amma zai yuwu a samu mafitar ta siyasa.”

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164