Da Duminsa: EFCC ta yi ram da Manajan Kamfanin Jirgin sama kan karkatar da kuɗaɗen mahajjata
- Hukumar EFCC ta kame Manajan Darakta na kamfanin jiragen sama Medview Airline, Mr. Muneer Bankole bisa zargin karkatar da kuɗin hajji
- Rahoto ya tabbatra da cewa Bankole ya isa hedkwatar EFCC tun karfe 11:00 na safiya Litinin, kuma ya sha tambayoyi daga jami'an hukuma
- Kakakin hukumar mai yaƙi da cin hanci da rashawa a Najeriya, Wilson Uwujaren, ya tabbatar da faruwar lamarin yayin da aka tuntuɓe shi
Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa, (EFCC) ta tsare Dataktan kamfanin jirgin sama, Medview Airline, Mista Muneer Bankole, kan zargin karkatar da kuɗin Hajji.
Daily Trust ta rahoto cewa Bankole, wanda ya isa Hedkwatar EFCC dake Abuja da misalin ƙarfe 11:00 na safiyar ranar Litinin, ya sha tambayoyi daga jami'an hukumar.

Source: UGC
Wata majiya dake da alaƙa da lamarin, ta shaida cewa hukumar yaƙi da cin hanci ta gayyaci Bankole ne kan zargin karkatar da kashi 50 cikin 100 na kuɗaɗen da aka ba shi.

Kara karanta wannan
2023: Ina da yakinin zan lallasa Atiku, Saraki, da sauransu a zaɓe, Ɗan takara ya bugi kirji
EFCC na zargin shugabam kamfanin jiragen saman da karkatar da kuɗaɗen da hukumar aikin Hajji ta ƙasa ta ba shi dan gudanar da aiki.
Kazalika ana zargin Bankole da wasu ƙarin dala dubu $900,000 da aka ba shi domin jigilar mahajjata a shekarar 2019, a cewar majiyar.
Punch ta rahoto majiyar ta ce:
"Hukumar Hajji ta ba shi kashi 50 na kuɗaɗen da kuma ƙarin $900,000 na jigilar mahajjata zuwa Saudiyya a 2019, amma bai yi aikin ba kuma ya gaza mauda kuɗin."
Rahoto ya nuna cewa hukumar na zargin ya karɓi makudan kuɗaɗen ya shirya amma bai aiwatar da aikin da aka ba shi ba.
Da muka tuntubi kakakin hukumar EFCC, Wilson Uwujaren, ya tabbatar da kame Darakta Muneer Bankole.
A wani labarin kuma Ɗan takarar shugaban ƙasa ya ce yana da kwarin guiwar zai lallasa Atiku, Saraki, Tambuwal da sauran su ya samu nasara
Fitaccen ɗan jarida kuma ɗan takarar shugaban ƙasa a PDP ya ce yana da tabbacin zai iya lallasa su Atiku, Saraki da sauran su.

Kara karanta wannan
Yanzu-Yanzu: Gwamnan PDP a Arewa ya bayyana shirin da yake na gaje kujerar Buhari a 2023
Dele Momodu,ya ce da yana tunanin ba zai iya nasara a zaɓen fidda gwani ba, da ba zai ayyana neman takara ba kwata-kwata.
Asali: Legit.ng