Babban abinda zai iya hana gudanar da babban zaben 2023, Shugaban INEC ya magantu

Babban abinda zai iya hana gudanar da babban zaben 2023, Shugaban INEC ya magantu

  • Shugaban INEC, Farfesa Mahmud Yakubu, yace ƙaruwar matsalar tsaro a Najeriya na cigaba da zama babban abin damuwa game da zaben 2023
  • Yakubu ya kuma yaba wa hukumomin tsaro bisa namijin kokarin da suka yi wajen tabbatar da tsaro yayin zaben Anambra
  • Yace a halin yanzu, INEC, ta sanya manyan zabukan jihohin Ekiti da Osun a gaba, da kuma zaɓen kananan hukumomin Abuja

Abuja - Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta (INEC), Farfesa Mahmud Yakubu, ya bayyana damuwarsa kan ƙaruwar matsalar tsaro yayin da zaben 2023 ke ƙaratowa.

Yakubu ya yi wannan furuci ne a wurin taron kwamitin tsaro na haɗin guiwa (ICCES), wanda ya gudana a hedkwatar hukumar INEC dake Abuja, kamar yadda Tribune Online ta rahoto.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun sake kai mummunan harin rashin imani jihar Neja, sun halaka dandazon mutane

Shugaban INEC, Mahmud Yakubu
Babban abinda zai iya hana gudanar da babban zaben 2023, Shugaban INEC ya magantu Hoto: @inecnigeria
Asali: Twitter

Shugaban INEC ya kuma yaba wa hukumomin tsaro bisa namijin kokarin da suka yi wajen tabbatar da tsaro yayin zaben gwamnan jihar Anambra.

Sai dai yace yawaitar matsalar tsaro a sassan Najeriya, wata barazana ce kuma abin damuwa game da zaɓen 2023.

Akwai aiki a gaban INEC - Yakubu

Kazalika, Farfesa Yakubu, ya bayyana zaɓen da hukumarsa ke fuskanta a cikin shekarar nan 2022 na wasu jihohin Najeriya.

Shugaban INEC yace:

"Game da zaben ƙarewar wa'adi, muna da manyan zaɓukan dake tafe cikin wannan shekarar 2022. Zaɓen gwamnan jihar Ekiti zai gudana ranar 18 ga watan Yuni, 2022 da kuma na jihar Osun ranar 16 ga Yuli, 2022."
"Sannan akwai zaben kananan hukumomi na Abuja da za'a gudanar nan gaba kaɗan. A mako mai zuwa kwamishinan zaɓe da na yan sanda za su mana bayani kan yanayin tsaro a faɗin Abuja."

Kara karanta wannan

Karin Labari: Gwamnan Arewa ya yi mubayi'a ga Tinubu, yace shi ya fi cancanta ya gaji Buhari a 2023

Daga cikin waɗan da suka halarci taron, akwai mai bada shawara kan tsaro, Babagana Monguno, darakatan hukumar DSS, Yusuf Magaji Bichi, da sufeta janar na yan sanda, Usman Baba.

A wani labarin na daban kuma Bola Tinubu ya bayyana babban abinda zai fara yi wa Talakawan Najeriya bayan zama shugaban ƙasa a 2023

Bola Tinubu, ya faɗi ɗaya daga cikin muhimman kudirinsa da zai fara aiwatar wa yan Najeriya da zaran ya zama shugaban ƙasa a 2023.

Tsohon gwamnan jihar Legas yace gwamnatinsa zata biya wa yara yan Sakandire kuɗin zana jarabawar WAEC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262