Gwamnoni za su sa kafar wando daya da Buhari a kan biyan tallafin fetur daga asusun FAAC
- Gwamnatocin jihohi ba su jin dadin yadda kamfanin NNPC ya ke rage abin da ake tarawa a FAAC
- Gwamnatocin tarayya, jihohi da kananan hukumomi su na da hakki da abin da ke cikin asusun
- Amma gwamnatin tarayya ta hannun NNPC ta na ragewa asusun tsoka, ta na biyan tallafin fetur
Abuja - Akwai alamu da ke nuna za a samu sabani tsakanin gwamnatin tarayya da jihohi a kan batun kason FAAC, Punch ta fitar da wannan rahoton.
Kwamitin asusun FAAC zai yi zaman farko na shekarar nan ta 2022 a ranar Laraba, 19 ga watan Junairu, 2022 domin a tattauna kan muhimman batutuwa.
Wasu jami’an gwamnati da suka zanta da jaridar Punch, sun koka a kan yadda kamfanin NNPC yake rage kason da ya kamata ya shigo asusun na FAAC.
Gwamnatocin jihohi ba su jin dadin yadda NNPC ke cire kaso mai tsoka domin a biya tallafin man fetur, don haka aka shirya za a warware wannan matsala.
An samu gibin N270bn
A halin yanzu NNPC na shirin cire N270.83bn daga kason da ya kamata a ce gwamnatocin tarayya, jihohi da kananan hukumomin sun raba a Junairu.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Za a cire wannan N270,831,143,856.56 ne saboda a cike gibin cinikin fetur da aka yi a watannin Nuwamban 2021 (N220.11bn) da Disamban 2021 (N50.720.bn).
Babu dalilin taba mani kudi
Kwamishinan kudi na Delta, Fidelis Tilije, ya ce kungiyarsu ta kwamishinonin kudi na jihohi ba su yarda NNPC ta rika taba wani abu daga asusun FAAC ba.
Fidelis Tilije wanda shi ne shugaban kungiyar kwamishinonin kudi na kasar nan ya ce dokar PIA ta bar nauyin tallafin man fetur a hannun tarayya ne ba FAAC ba.
Wannan shi ne ra’ayin irinsu kwamishinan kudi na jihar Ekiti, Akin Oyebode, wanda ya ce gwamnatin tarayya na taba asusun FAAC ne ba da izinin jihohi ba.
Za a zauna a makon nan
Kwamishinan kudi na jihar Kuros Riba, Asuquo Ekpenyong ya shaidawa manema labarai cewa kwamitin na FAAC zai zauna daga Laraba zuwa Alhamis dinnan.
Mai magana da yawun bakin NNPC, Garba-Deen Mohammad ya bayyana cewa lamarin tallafin fetur ya fi karfinsu, ya ce gwamnatin tarayya ke da iko kan wannan.
Bashin kudin fansho
A makon da ya gabata ne aka ji cewa Gwamnatin Muhammadu Buhari za ta ci bashin fiye da Naira Biliyan 600 daga asusun fanshon ma'aikatan gwamnatin tarayya.
Najeriya za ta karbi aron ne domin ana bukatar a kashe Naira tiriliyan 7.7 wajen gina hanyoyi, tituna da kuma sauran abubuwan more rayuwa tsakanin 2021 da 2025.
Asali: Legit.ng