Najeriya ce ta 8 cikin jerin kasashen duniya 162 da akafi kashe-kashen mutane, Ga jerin
Najeriya ta zamto ta takwas cikin jerin kasashen duniya 162 da ake fama da matsalar kashe-kashen mutane, bisa rahoton binciken Early Warning Project.
Wannan rahoto da aka saki ranar Alhamis ya nuna kasashen da aka fi Najeriya kisa sune Pakistan, India, Yemen, Afghanistan, DR Congo, Guinea, da Ethiopia.
Early Warning Project wani aikine na hadin kan cibiyar hana kashe-kashen Simon-Skjodt dake AMurka da cibiyar Dickey dake kwalejin Darmouth.
Za'a samu karin kashe-kashe a Najeriya a 2022
Rahoton ya yi hasashen cewa za'a samu karin kashe-kashe a Najeriya a 2022.
Wani sashen rahoton yace:
"Lissafinmu ya nuna cewa akwai yiwuwan a samun sabbin kashe-kashen 7.1% a Najeriya a 2021 ko 2022. Najeriya ce ta takwas cikin kasashe 162."
Ga jerin kasashe 30 da akafi kashe-kashe a duniya:
1 – Pakistan
2 – India
3 – Yemen
4 – Afghanistan
5 – DR Congo
6 – Guinea
7 – Ethiopia
8 – Nigeria
9 – Sudan
10 – Chad
11 – Somalia
12 – Turkey
13 – Libya
14 – Syria
15 – Iraq
16 – South Sudan
17 – Burma/Myanmar
18 – Jamhuriyyar Congo
19 – Thailand
20 – Central African Republic
21 – Burundi
22 – Mozambique
23 – Uganda
24 – Mali
25 – Tanzania
26 – China
27 – Indonesia
28 – Angola
29 – Kenya
30 – Iran
Asali: Legit.ng