Ba zan bar masu hannu a kisan dalibin kwalejin Dowen, Oromoni, su ci bulus ba, Shugaba Buhari
- Shugaba Buhari ya yi Allah wadai da kisan ɗalibin makarantar Dowen, Sylvester Oromoni, dake jihar Legas
- Buhari ya bayyana cewa gwamnatinsa ba zata bar duk me hannu a wannan kisan ɗalibin yaci bulus ba
- Ya bukaci yan sanda su cigaba da aikin bincike don gano asalin waɗan da suka kitsa lamarin su fuskanci fushin doka
Abuja - Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya tabbatar da cewa doka zatai aiki a kan duk wani mai hannu a kisan ɗalibin kwalejin Dowen, Sylvester Oromoni.
Ya bayyana cewa a yan kwanakin nan, ƙasar nan ta girgiza da mummunan lamarin da ya faru a kwalejin Dowen dake jihar Legas.
Shugaban ya yi wannan furuci ne a wata sanarwa da babban hadiminsa, Malam Garba Shehu ya fitar a shafinsa na Facebook.
Buhari ya yi Allah wadai da kisan da akaiwa Oromoni, ɗaya daga cikin ɗalibai masu hazaka dake jan zarensu a makaranta, kuma yake sanya iyalansa farin ciki.
A cewarsa idan har wannan abun yana da alaƙa da kungiyoyin asiri ko zalunci, to zai zama tamkar ɗana kunamar bindiga na kawo karshen faruwar irin haka baki ɗaya.
Buhari ya yi jimami
Shugaba Buhari yace:
"Na kadu sosai kuma naji ko ina ya ɗau zafi biyo bayan faruwar lamarin. A madadin ni kaina, iyalaina, da gwamnatin Najeriya muna mika ta'aziyyar mu ga iyalan Oromoni, gwamnati da mutanen Legas."
"Kuma ina mai tabbatar muku cewa za'a gudanar da tsattsauran bincike kan abinda ya faru kuma zamu tabbatar da hukunta duk wanda keda hannu."
Buhari ya umarci yan sanda su cigaba da bincike
Shugaban ƙasa ya kuma bukaci yan sanda su cigaba da aikin bincike har sai sun gano tun daga inda aka kitsa lamarin domin doka ta yi aikinta.
Ya kuma kara bada tabbacin cewa wajibi ne a ɗauki matakin kan koma waye me hannu a wannan kisan.
A wani labarin kuma Mutane sun yi gudun mutuwa yayin da wata kotu ta rushe ana tsaka da zaman Shari'a
Mutane sun yi gudun tsira da rayuwarsu yayin da rufin ginin wata kotu ya fara rushewa ana tsaka da zaman shari'a.
Rahotanni sun bayyana cewa lauyoyi, ma'aikatan kotu da waɗan da ake tuhuma sun yi kokarin fita domin tsira.
Asali: Legit.ng