Mataimakin Shugaban kasa ya bayyana abin da zai faru idan aka yi gigin barka Najeriya
- Yemi Osinbajo ya zauna da kungiyar Muhammadu Buhari Osinbajo Dynamic Support Group a Aso Rock
- Farfesa Yemi Osinbajo ya fadawa ‘yan kungiyar magoya-bayan muhimmancin hadin-kan Najeriya
- Mataimakin shugaban kasar yace kuskure ne a raba kasar nan, yace hakan zai sa talauci ne ya karu
Abuja - Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo yace matsalolin da suka damu Najeriya irinsu talauci, za su ninku idan har aka raba kasar nan.
Da yake magana a birnin tarayya Abuja, jaridar Daily Trust ta rahoto Farfesa Yemi Osinbajo ya na cewa za a shawo kan kalubalen da ake fuskanta ba da dadewa ba.
Yemi Osinbajo ya yi wannan jawabi yayin da ya gana da wakilan kungiyar Muhammadu Buhari Osinbajo (MBO) Dynamic Support Group a fadar Aso Rock Villa.
Mataimakin shugaban Najeriyar ya fadawa kungiyar magoya bayan na su cewa gwamnati za ta magance matsalar rashin tsaro, kuma Najeriya za ta dawo da karfinta.
Rahoton yace jawabin mai girma mataimakin shugaban kasar ya fito ne ta bakin Laolu Akande.
Muhimmancin hadin-kai da zaman lafiyan Najeriya
Laolu Akande yace Farfesa Osinbajo ya jaddada muhimmancin a samu hadin-kai a Najeriya, inda ya kore kiran da wasu suke yi a halin yanzu na cewa a barka kasar.
“Ka da mu yi kasa a gwiwa wajen tabbatar da cewa mun tsare kasar nan, kuma ka da mu saki hanya daga manufar da muke kokarin mu cin ma.”
“Shugaban kasa ya tsaya tsayin-daka wajen magance matsalolin kasar nan, kama daga rashin tsaro; da gaske yake yi, babu abin da ke dauke masa hankali.”
“Masu bada shawarar kasar nan ta barke, ko menene dalilinsu kuwa, sun yi kuskure kuma dole ne mu fada masu wannan a kullum.” – Yemi Osinbajo.
Farfesa Osinbajo yace hadin-kan kasar nan ya na da amfani ga kowace kabila, addini da kuma kowa.
“Kasar da ita ce gaba wajen karfin tattalin arziki a Afrika za ta zama daya daga cikin manya a Duniya, idan aka fara datsa ta, matsaloli za su nunku.”
Siyasar jam'iyyar APC
Ana jin kishin-kishin APC na daf da sa ranar da za ta zabi shugabannin din-din-din da za su canji kwamitin rikon kwarya da gwamna Mai Mala Buni yake jagoranta.
Bayan shekara daya da rabi, kwamitin rikon kwarya ne yake rike da shugabancin jam’iyyar APC. Tun 2018 ne APC tayi zaben karshe, aka nada Adams Oshiomhole.
Asali: Legit.ng