COVID-19: Gwamnatin Buhari ta kashe Naira Biliyan 9.9 a kan wanke hannuwa a 2021
- Femi Falana SAN ya aika takardar FOI, ya na neman diddikin yadda aka kashe tallafin COVID-19
- Gwamnatin tarayya ta aiko masa takarda, ta ba shi amsar inda aka kai wadannan tiriliyoyin kudi
- Matasa sun samu kaso mai yawa daga cikin kudin da gwamnati ta rabawa ma’aikatu da ‘yan kasuwa
Abuja - Gwamnatin tarayya ta karkashin ma’aikatar ruwa, ta batar da Naira biliyan 9.9 a wajen dabbaka shirin ‘wanke hannu’ daga tallafin cutar COVID-19.
Punch tace kusan Naira biliyan 10 na kason ma’aikatar na tallafin yaki da annobar cutar Coronavirus a shirye-shiryen tsabtace ruwa da kiwon lafiya.
Haka zalika an ware Naira biliyan 94 domin horas da matasa, a kuma sama masu aikin yi.
Ma’aikatar tattali, kasafi tsare-tsaren arziki ta bayyana wannan bayan shahararren lauya, Femi Falana ya aika mata takardar FOI, ya na neman wasu bayanai.
Dr. Zakari Lawal ya sa hannu a amsar takardar da Femi Falana SAN ya aiko, ya na neman jin yadda gwamnati ta kashe Naira tiliyan 1.5 na tallafin COVID-19.
2021: FEC ta amince a batar da N1.9tr
A tsakiyar 2020 majalisar zartarwa ta amince a kashe Naira tiriliyan 2.3 domin tallafawa tattalin arzikin Najeriya. An raba kudin ne ga ma’aikatu da kamfanoni.
InfoDig tace tuni dai gwamnati ta raba Naira tiriliyan 1.9 daga cikin wadannan kudi. A ciki matasa suka samu N94bn, aka kuma saye kayan aiki na N128.5bn.
Ma’aikatar matasa da cigaban wasanni ta samu N690m, wanda ta horas da matasa 300 kan harkar fasahar noma da ilmin samar da wuta daga hasken rana.
Sauran ma'aikatun da suka ci moriyar kudin
Baya ga haka, ma’aikatar ta samu N3.1bn da nufin a horas da matasa 4300 a kan fasahar ICT. An kashe kudin ne a Kano, Bauchi, Filato, Osun da wasu jihohi 24.
Rahoton yace ma’aikatar sadarwa ta samu N1bn, ma’aikatar mata ta ci N1.250b duk daga wannan kudin. An kuma ba NDE N52bn domin koyawa matasa kasuwanci.
‘Yan kasuwa sun samu N49bn, sauran ma’aikatun da suka amfana su ne; na tattalin arziki, harkar gona, jiragen sama. Sai kuma hukumomi irinsu REA, REA, da FMBN.
Facakar gwamnatin Najeriya wajen sayen motoci
Kun ji cewa bashin da ake bin Najeriya ya haura Naira Tiriliyan 33 a halin yanzu, amma gwamnatin tarayya tana kara ware kudi domin a sayo wasu motoci.
Kudin da fadar shugaban kasa ta batar a sayen motoci daga shekarar 2015 zuwa yanzu, sun isa a gina kananan asibiti 13 a kowace Jiha da babban birnin tarayya Abuja.
Asali: Legit.ng