Hukumar kwastam ta tattarowa Gwamnati Naira Biliyan 86 a tashar Apapa a kwana 30
- Jami’an hukumar kwastam da ke aiki a tashar Apapa sun tara N86bn a cikin watan Oktoban 2021.
- Ma’aikatan kwastam sun rika samun kusan Naira biliyan uku a duk rana a iyakar ta jihar Legas.
- Shugaban jami’an da ke yaki da masu fasa-kauri a reshen Apapa, Malanta Yusuf ya bayyana haka.
Lagos - Jami’an hukumar kwastam masu yaki da fasa-kauri na reshen Apapa, jihar Legas, sun ce sun samu sama da Naira biliyan 80 a watan da ya gabata.
Daily Trust ta rahoto jami’an kwastam da ke tashar Apapa suna cewa sun tattaro Naira biliyan 86.023 a cikin watan Oktoba duk da matsalolin da suka samu.
Hukumar kwastam ta reshen Apapa ta samu wannan kudi ne a sanadiyyar sababbin dabarun tara kudin shigar da shugabanta, Malanta Yusuf, ya shigo da su.
A wannan lokaci, kwastam ta dage wajen samun hadin-kai tsakaninta da sauran hukumomin gwamnati, da kuma samun yardar sauran masu ruwa da tsaki.
Malanta Yusuf ya jagoranci aikin kwastam
Malanta Yusuf ya yi bayanin yadda aka samu wadannan kudi, yace Naira biliyan 44.6 sun fito ne daga kudin shigo da kaya daga kasashen waje da harajin CET.
Kwastam sun samu Naira biliyan 18.8 daga kudin tashar ruwa. Sauran kason sun fito ne daga harajin shigo da sukari, fulawa, da karafuna daga kasashen waje.
Haka zalika jami’an na kwastam da ke kula da tashar Apapa suna karbar kudin CISS, NAC, da ETLS. Sannan ana karbar kudi a hannun masu shigo da alkama.
Rahoton The Nation yace jami’an sun karbi sama da Naira biliyan 22 a matsayin kason haraji na VAT.
Shugaban hukumar na wannan reshen, Malanta Yusuf yace za su cigaba da yin bakin kokarinsu wajen sauke nauyin da yake kansu na tsare tattalin arzikin kasa.
Yusuf yace ba za su yi wasa da aiki ba, kuma za su kama duk wanda aka samu da laifin fasa-kauri, ko kwastam ta karbe kaya idan bukatar yin hakan ta tashi.
Kwastam tana harin N2tr a 2022
A makon jiya aka ji cewa shugaban kwastam na kasa, Hameed Ali zai tarawa Gwamnatin Muhammadu Buhari harajin Naira Tiriliyan 2 cikin shekarar badi.
Kusan 80% na wannan kudi za su fito ne daga kan iyakokin kudu maso yamma, musamman Legas. Abin da za a samu daga iyakokin Arewa ba su zarce 4% ba.
Asali: Legit.ng