Kudin da kamfanin simintin Dangote PLC ya samu a shekarar 2021 ya zarce N1.02tr

Kudin da kamfanin simintin Dangote PLC ya samu a shekarar 2021 ya zarce N1.02tr

  • Kamfanin Dangote Cement Plc ya samu kazamar riba daga watan Junairu zuwa Satumban 2021.
  • A cikin watanni tara, kamfanin simintin ya samu Naira Tiriliyan 1.02 da ribar Naira biliyan 450.5.
  • Shugaban kamfanin Dangote Cement Plc, Michel Puchercos ya fitar da alkaluman shekarar nan.

Lagos-Kamfanin Dangote Cement Plc wanda shi ne babban kamfanin siminti a fadin Afrika, ya fito da rahoton kudi da ribar da ya samu a shekarar nan.

Daily Trust ta fitar da rahoto a ranar Litinin, 1 ga watan Nuwamba, 2021, cewa abin da kamfanin mai fitar da 48.6Mta a duk shekara, yake samu, ya karu.

Alkaluma sun nuna kamfanin ya samu Naira tiriliyan 1.02 daga watan Junairu zuwa Satumban bana. Bayan cire haraji, an samu ribar Naira biliyan 405.5.

Kara karanta wannan

Dinbin mutane sun makale carko-carko yayin da gini mai hawa 20 ya ruguje a Najeriya

Hakan ya nuna Dangote Cement Plc ya samu karin kashi 34.2% da 49.1% na kudi da riba a bana.

Duk da matsalar ruwan sama, wanda ya jawo aka rage gine-gine daga Yuli zuwa Satumba, Dangote ya saida siminti tan miliyan 14.1 a wannan lokaci.

Kamfanin simintin Dangote
Simintin Dangote Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ciniki ya karu duk da damina

Rahoton yace kamfanin na Dangote Cement Plc ya gamu da karin kasuwa na kashi 18.7%.

Alkaluman sun kuma tabbatar da cewa a Najeriya ne kamfanin ya fi saida buhunan siminti. Dangote Cement Plc ya samu 63.5% na cinikinsa a kasar nan.

Duk da irin kudin da ake samu a Najeriya, 58.3% na adadin simintin da ya kamata ake samarwa. Kamfanin da ke Legas zai iya hada tan miliyan 32 a shekara.

Daga cikin abubuwan da suka jawo ribar kamfanin yake karuwa akwai nasarar da aka ci wajen fara gina titi da siminti bayan tsawon lokaci ana wannan kira.

Kara karanta wannan

Kasafin 2022: Ta kacame tsakanin sanatoci kan raba wa mazabu ayyukan tituna

Shugaban kamfanin Dangote Cement Plc, Mista Michel Puchercos ya yaba da sakamakon da aka samu. Sai dai kamfanin suna fuskantar takara a kasar Ghana.

Farashin kayan abinci zai tashi

Dazu kun ji rahoto cewa karancin ruwan sama, tsadar iri da takin zamani, da ambaliyar ruwa da wahalar ban ruwa za su jawo tsadar abinci na masifa a 2022.

A wasu Jihohin an samu amfanin gona, amma an rufe kasuwanni saboda matsalar tsaro. Shi ma wannan ya sa ake ganin cewa kayan abinci za su kara tsada.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng