Kungiyar Kiristoci, PFN ta bukaci Gwamnati ta kama Malamin Musulunci, Ahmad Gumi

Kungiyar Kiristoci, PFN ta bukaci Gwamnati ta kama Malamin Musulunci, Ahmad Gumi

  • Pentecostal Fellowship of Nigeria ta bada shawarar a damke Sheikh Ahmad Gumi
  • Kungiyar kiristocin tace ya kamata a kama malamin saboda irin kalaman da yake yi
  • Archbishop John Osa-Oni ya bayyana wannan a lokacin da PFN ta shirya wani taro

Lagos - Kungiyar kiristoci na Pentecostal Fellowship of Nigeria, PFN, ta yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kama Sheikh Ahmad Gumi.

PFN ta reshen kudu maso yammacin Najeriya tana so a damke babban malamin addinin musuluncin ne saboda maganganun da yake yawan yi.

The Guardian tace kalaman da shehin malamin ya yi kwanan nan, inda yace ka da a ayyana ‘yan bindiga a matsayin ‘yan ta’adda ne ya jawo wannan kira.

Kungiyar kiristocin tace babban malamin ya kamata a fara kamawa da zargin alaka da ‘yan bindiga.

Kara karanta wannan

Kotu ta ɗaure wani matashi da ya yi asubanci ya tafi coci ya sace kujerun roba

Jaridar News Digest tace kungiyar PFN ta dauki wannan matsaya a wajen wani taro da ta shirya a garin Legas a ranar Talata, 26 ga watan Oktoba, 2021.

Ahmad Gumi
Dr. Ahmad Abubakar Mahmud Gumi Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Archbishop John Osa-Oni ya yi magana

Taron ya samu halartar wakilan kungiyar addinin daga jihohin Oyo, Osun, Ondo, Ogun da Ekiti.

Shugaban kungiyar na reshen kudu maso yamma, Archbishop John Osa-Oni yace akwai alamar tambaya a game da kalaman da ke fitowa daga bakin shehin.

Archbishop John Osa-Oni yace da a ce Sheikh Ahmad Gumi jagoran addinin kirista ne, da tuni an kama shi. Faston ya na mai nuna akwai son kai a lamarin.

Da yake jawabi a madadin Pentecostal Fellowship of Nigeria, John Osa-Oni yace ya kamata gwamnatin tarayya ta kama malamin domin a hukunta shi.

A na sa bangaren, babban faston nan na Legas, Dr. Alfred Martins, ya yi kira ga gwamnati tayi bakin kokarinta wajen kawo karshen matsalar rashin tsaro.

Kara karanta wannan

CAN ga FG: Ya kamata a garkame Sheikh Gumi saboda yiyuwar alaka da 'yan bindiga

'Yan bindiga sun addabi Sokoto

A makon nan aka ji cewa 'yan bindiga suna umartar mazauna wasu kauyuka su tara masu kudi a wasu garuruwan Sokoto, idan ba haka ba za a kawo masu hari.

An haramtawa mutane zuwa gona har sai sun biya kudin da aka bada umarni. Rashin tsaro ya sa jama’a na tara kudi su bada domin jami’an tsaro ba su da tabbas.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng