‘Yan bindiga sun sa 'yan gari su tara masu kudi nan da Juma’a ko a kawo masu hare-hare

‘Yan bindiga sun sa 'yan gari su tara masu kudi nan da Juma’a ko a kawo masu hare-hare

  • ‘Yan bindiga sun daura harajin dole a kan wasu kauyuka da ke jihar Sokoto
  • An addabi Attalawa, Danmaliki, Adamawa, Dukkuma, Sardauna da Dangari
  • Mutane na biyan kudin ko su bar gari saboda su gujewa harin ‘yan bindiga

Sokoto - ‘Yan bindigan da suka addabi yankin gabashin jihar Sokoto sun sa haraji a kan mutanen kauye, sun bukaci a kawo masu kudi, ko a kawo masu hari.

Wani rahoto da Daily Trust ta fitar, ya nuna an ba mazauna yankin nan da ranar Juma’a, 29 ga watan Oktoba, 2021, su biya wadannan kudi da aka bukata.

‘Yan bindigan sun hana mutanen kauyuka shiga gonakinsu, har sai sun tara masu wadannan kudin.

Wani mazaunin yankin ya shaidawa manema labarai cewa wasu sun fara biyan kudin da aka sa masu, wasu kuma suna bakin kokari kafin wa’adin ya cika.

Kara karanta wannan

Miyagun yan bindiga sun sake kai sabon hari jihar Zamfara, Sun kashe Mutane

Sahara Reporters tace ‘yan bindigan suna la’akari da girman kauye wajen yankawa al’umma harajin na su.

Aminu Tambuwal
Gwamnan Sokoto, Aminu Tambuwal Hoto: premiumtimesng.com
Asali: Facebook

Kauyukan da ‘yan bindiga suka addaba

“An ce wasu su biya N400, 000, wasu kuma za su biya N700, 000, wasu kuma za su biya abin da bai kai haka ba. Ya ragewa mutane su san yadda za su yi.”
“A wasu kauyukan, an ce masu gida su kawo N2, 000, matasan da ba su da aure sai su biya N1, 000.” – Majiya.

‘Yan bindigan sun bukaci a hada masu N400, 000 a kauyukan Attalawa, Danmaliki, Adamawa, Dukkuma, Sardauna da Dangari, za a biya kudin nan da Juma’a.

Babu yadda aka iya – ‘Dan Majalisan Sokoto

‘Dan majalisar dokokin jiha mai wakiltar mazabar Sabon Birni ta Arewa, Hon. Aminu Almustapha Gobir yace ana kai masu hari saboda sun ki biyan kudin.

Kara karanta wannan

Sabon hari: 'Yan bindiga sun kai hari masallaci, sun bindige masallata a jihar Neja

“Mutane sun gwammace su biya kudin su zauna lafiya a kauyukansu, da su dogara da jami’an tsaro, ko kuma su tsere daga yankin.” – Hon. Aminu Gobir

Duk da haka akwai lokutan da aka biya kudin, kuma hakan bai hana ‘yan bindiga su kawo hari ba.

Yaudarar Igboho aka yi - Adeyeye Ogunwusi Ojajaya

Kwanan nan ne Ooni na kasar Ife, Adeyeye Ogunwusi Ojajaya fito ya yi magana game da Sunday Igboho, yace wasu ‘Yan siyasa ne suka kai shi, suka baro shi.

Yanzu Igboho ya shiga hannu amma duk da haka Adeyeye Ogunwusi Ojaja II yace sun yafe masa, kuma suna kokarin ceto shi daga inda yake tsare a kasar Benin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng