El-Rufai ya rubuta wasika, yana so a ayyana ‘Yan bindigan Arewa a matsayin ‘yan ta’adda
- Malam Nasir El-Rufai yana so Gwamnatin Najeriya ta sa wa ‘Yan bindiga jar alama
- Gwamnan yace tun a 2017 yake so a ayyana ‘Yan bindigan a matsayin ‘yan ta’adda
- El-Rufai ya bayyana cewa yin wannan zai ba Sojoji dama su iya kashe ‘yan bindigan
Kaduna - Malam Nasir El-Rufai ya yi kira ga gwamnati ta ayyana miyagun ‘yan bindigan da suka addabi Arewa maso yammacin kasar nan a matsayin ‘yan ta’adda.
Jaridar Daily Trust ta rahoto gwamnan jihar Kaduna yana so a jefa wadannan ‘yan bindagan a rukunin ‘yan ta’adda ko kuma masu tada kayar baya a Najeriya.
Gwamnan ya bayyana cewa yin hakan zai taimaka sojojin Najeriya su hallaka duk wani ‘dan bindiga da aka kama, ba tare da jawo fushin kasan Duniya ba.
Gwamnan ya bayyana wannan ne bayan ya karbi rahoton sha’anin tsaro da kwamishinan tsaro da harkokin gida na Kaduna, Samuel Aruwan ya gabatar masa.
Rahoton yace Mista Samuel Aruwan ya gabatar da wannan rahoto ne a gidan gwamnati na Sir Kashim Ibrahim House, a ranar Laraba, 20 ga watan Oktoba, 2021.
Har ila yau, gwamna El-Rufai yace daukar matasa 1, 000 a kowace karamar hukuma a kasar nan zai taimaka sosai wajen kawo karshen ta’adin ‘yan bindigan.
Ina tare da Majalisar Tarayya - Nasir El-Rufai
Mai girma Nasir El-Rufai ya na tare da ‘yan majalisar tarayya da suka bukaci a ayyana miyagun da ‘ya ta’adda. El-Rufai ya gabatar da wannan roko tun a 2017.
“Mu a gwamnatin jihar Kaduna, muna kira ga gwamnatin tarayya ta ayyana ‘yan bindiga da ‘yan bindiga kuma masu tada kafar baya.”
“Mun rubuta wasika zuwa ga gwamnatin tarayya tun shekarar 2017, muna so a yi wannan ayyana wa.” - Malam Nasir El-Rufai
“Saboda yin hakan zai bada dama sojoji su kashe wadannan ‘yan bindiga ba tare da tsoron saba dokokin kasashen waje.”
Dazu kun ji cewa Hafsun Sojan kasa, Janar Farouk Yahaya ya jinjinawa Sojojin da suka kashe ‘Yan Boko Haram a wasu hare-hare da aka kai a kauyukan Borno.
Kakakin sojojin kasa, Janar Onyema Nwachukwu ya fitar da wani jawabi a ranar Talata, 19 ga watan Oktoba, 2021, yana bayyana nasarorin da sojoji suka samu.
Asali: Legit.ng