Sababbin bayanai sun fito a kan zargin da ake yi wa Sanata Ekweremadu da Matarsa a Ingila
- Ike Ekweremadu ya rubutawa hukumomin Birtaniya takarda kan dasher kodar da za ayi wa ‘yarsa
- Tsohon shugaban majalisar dattawan ya sanar da ofishin jakadancin Birtaniya wannan tun 2021
- Amma ana zargin Sanatan ya boye gaskiyar shekarun wannan yaro da ya dauko daga gidan talakawa
United Kingdom - Tsohon shugaban majalisar dattawan Najeriya, Ike Ekweremadu ya yi karin-haske a kan zargin da hukumomin Birtaniya suke yi masa.
Jaridar The Cable ta ce Sanata Ike Ekweremadu ya yi ikirarin ya rubutawa ofishin jakadancin Birtaniya takarda a game da dashen kodar da za ayi wa diyarsa.
Ekweremadu ya sanar da kasar Birtaniya tun a watan Disamban 2021 cewa zai dauki nauyin bizar wanda zai bada kodar da za a dasawa Ms Sonia Ekweremadu.
Zunuban Ike Ekweremadu: Manyan rigingimu 4 da tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawan ya fada ciki
Kamar yadda ya rubuta a wasikar, tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawan na Najeriya ya yi bayanin za ayi aikin ne a asibitin Royal Free a birnin Landan.
Sanatan na Enugu ya ce shi zai biya duk wasu kudi da za a bukata wajen yin dashen kodar yarinyar.
Har ila yau, Ekweramadu ya hadawa ofishin jakadancin kasar Birtaniya takardar asusun bankinsa. Legit.ng Hausa ta samu ganin wannan takarda a dazu.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Bugu da kari, a karshen wasikar da ya aika a shekarar da ta wuce, Sanatan na yammacn Enugu ya ce idan akwai wani bayani da ake bukata, za a iya tuntubar shi.
Bayan kusan watanni shida da rubutawa Birtaniya wannan takarda, sai ga shi jami’an kasar Ingilan sun yi ram da ‘Dan siyasan tare da mai dakinsa, an garkame su.
Ana zargin Ekweremadu da Beatrice Nwanneka Ekweremadu mai shekara 55 da neman cire kodar mutum.
Rahoton da Arise TV ta fitar dazu ya bayyana cewa yaron da tsohon shugaban majalisar dattawan ya kawo ‘dan shekara 15 ne, amma sai ya yi karyar cewa ya kai 21.
'Dan majalisar ya yi wa wannan karamin yaron da bai da wurin zama alkawarin cewa rayuwarsa za ta canza idan aka dace, baya ga takardun karya da aka yi masa.
Sanata ya shiga hannu
Tun dazu da yamma ku ka ji labari cewa an damke Sanata Ike Ekweremadu da matarsa a kan kokarin kai wani yaro kasar Birtaniya da nufin a saci sashen jikinsa.
'Yan sandan Birtaniya sun ce an garkamesu a kurkuku kuma za su gurfana a kotu a yau dinnan. Daga baya labari ya zo cewa Alkali ya ki amincewa ya ba su beli.
Asali: Legit.ng