Hazikin mutumin Najeriya mai Digiri 7, ya koma makaranta ya yi sabon Digirin PhD
- Wani mutumi mai ‘dan karen sha’awar karatun boko, mai suna Temitayo Bello ya yi digirin PhD biyu
- Dr. Temitayo Bello ya na da digiri a fannin tattalin arziki, ilmin shari’a, aikin banki, da ilmin komfuta
- Bello ya yi karatunsa ne a jami’o’in Ogun, Osun, Ibadan da Legas, sannan ya fita har kasar Birtaniya
Wani mutumin Najeriya, Temitayo Bello ya kammala karatunsa na digirin PhD, bayan tulin digiri da ya tara a jami’o’in gida da na ketare.
Jaridar Daily Trust ta kawo labarin wannan Bawan Allah, Temitayo Bello, wanda yanzu yana da digiri bakwai a fannoni da dama na ilmi.
Wannan digiri na PhD da Dr. Temitayo Bello ya yi, shi ne na biyu da ya samu a rayuwarsa. Bello ya tara digiri iri-iri da satifiket daga jami’o’i.
Bello ya yi digirinsa na uku na zama Dakta ne a bangaren shari’a a jami’ar Ibadan. Kafin nan ya taba yin digirin na PhD, ya kuma zama Dakta.
Rahoton yace digir-digiri din da Bello ya yi a baya a fannin huldar kasashen Duniya da shari’a ne.
Daya daga cikin ‘ya ‘yan wannan ‘dan boko, Titilola Bello ya bada sanarwar nan a shafinsa na LinkedIn, yace mahaifinsa ya kammala PhD.
Titilola Bello yace mahaifinsa ya yi digiri da-dama, daga ciki akwai wasu a bangaren ilmin tattalin arziki, aikin banki da ilmin komfuta.
Titilola Bello a LinkedIn
“Wannan kari ne a kan PhD da yake da shi a huldar kasashen Duniya da shari’a, Masters a ilmin shari’a da digirin M.Sc a ilmin tattalin arziki.”
“Da M.Sc a ilmin tattali da aikin banki, M.Sc a ilmin komfuta, digirin LLB da BL a harkar shari’a, da B.Sc a fannin ilmin tattalin arziki.”
Baya ga haka, Bello ya yi digirin farko a tattali da aikin banki da kuma PGD a ilmin komfuta.
Temitayo Bello ya yi karatunsa ne a jami’ar Landan, UNILAG, jami’ar Ibadan, jami’ar aikin gona ta Abeokuta, Babcock da kuma jami’ar jihar Osun.
Yajin-aikin ASUU
Malaman Jami’a sun yi karin haske a game da shirin sake rufe makarantun jami'o'i. Hakan na zuwa ne bayan dogon yajin-aikin da aka yi a shekarar 2020.
Shugaban ASUU, Farfesa Emmanuel Oshodeke yace har yau ba su ji daga bangaren gwamnati ba
Asali: Legit.ng